Kano: Ganduje ya dauka tsatsauran mataki a kan karin farashin kayayyaki

Kano: Ganduje ya dauka tsatsauran mataki a kan karin farashin kayayyaki

- Sanannen abu ne idan aka ce 'yan kasuwa na kara farashin kaya idan watan Ramadan ya iso

- Hakan ce ta kasance a jihar Kano tun bayan saka dokar takaita zirga-zirga a jihar da kuma isowar Ramadan

- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kafa kwamitin da ya daidaita farashin kayayyaki a kasuwannin jihar

A jihar Kano da sauran jihohin yankin Arewacin Najeriya, masu saida kayayyaki na ganin watan azumi a lokacin da suke tara riba da yawa. Su kan kara kudin kayayyakin ba kamar yadda suka saba siyarwa ba.

Duk da jama'a da malamai na iyakar kokarinsu wajen ganin an wa'azantar da 'yan kasuwar a kan illar hakan, suna ci gaba da cin karensu babu babbaka.

Ba zato, sai 'yan kasuwar suka fara amfani da kullen COVID-19 wajen kara farashin kayayyakin bukata ta yadda farashin ya kazanta. Lamarin ya kai ga an samu karin farashin da kashi 200 a cikin kwanaki kalilan.

A saboda haka, hankalin jama'a ya tashi don ba kowa ke iya cin abinci ba. Jama'ar jihar sun yi kira ga gwamnati da su tallafa musu don shawo kan wannan matsala, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Kano: Ganduje ya dauka tsatsauran mataki a kan karin farashin kayayyaki
Kano: Ganduje ya dauka tsatsauran mataki a kan karin farashin kayayyaki
Asali: Twitter

KU KARANTA: An damke malamin da ya yi wa El-Rufai 'wankin babban bargo' a kan hana sallar Idi

A yayin martani a kan wannan koken, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umarci hukumar yaki da rashawa ta jihar da ta dauka matakan da suka dace.

A yayin aiki a kan umarnin, shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado ya fitar da hanyoyin daidaita farashin kayayyaki a jihar.

A ranar farko da aka fara binciken, an garkame wuraren adana kayayyaki masu tarin yawa. An gano cewa 'yan kasuwar ke boye kayayyaki wadanda aka bankado daga baya.

Daga baya, Gado ya yi taro da kungiyar 'yan kasuwa ta jihar sannan suka samu matsaya.

Bayan kammala taron, Gado ya bayyana cewa, "Mun daidaita da su. Buhun shinkafa babba ya koma N16,000 kuma ba za su dinga boye kaya ba."

Kamar yadda ya bayyana, dukkan farashin kayayyaki an daidaita su hatta ruwan leda wanda ya koma N120, ya koma N80.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel