Dalilinmu na yin Sallar Idi ranar Juma'a bayan yin azumi 29 - 'Yan Shi'a

Dalilinmu na yin Sallar Idi ranar Juma'a bayan yin azumi 29 - 'Yan Shi'a

A ranar Juma'a, 22 ga watan Mayu, mabiya Shi'a a Najeriya su ka gudanar da shagulgulan bikin Sallah bayan sun yi Sallar Idi.

Sidi Manniru, shugaban mabiya Shi'a a jihar Sokoto, ya ce sun yi sallar Idi ranar Juma'a ne saboda sun ga jaririn watan Shawwal ranar Alhamis bayan sun yi azumi 29.

A hirarsa da wakilin jaridar Aminiya, Manniru ya ce mutanen da su ka yarda da su sun sanar da su cewa an ga jaririn watan Shawwal a garin Dukkuma a yankin karamar hukumar Isa da garuruwan Yabo da Illela dukkansu a jihar Sokoto.

Da ya ke amsa tambaya a kan ko sun sanar da sarkin Musulmi labarin ganin watan, sai ya ce, "tun kimanin fiye da shekaru 20 da su ka wuce mu ke da tsari na duba wata, ba sai iya watan Ramadan ba.

"Mun yi hakan ne don kaucewa rudanin da ake samu a Najeriya dangane da ganin wata. Mu na da mutanenmu a ko ina, kuma mu tamkar tsintisya mu ke; madaurinmu daya, da zarar 'yan uwanmu sun sanar da mu ganin wata, babu sauran wata jayayya."

Dalilinmu na yin Sallar Idi ranar Juma'a bayan yin azumi 28 - 'Yan Shi'a
Sallar Idin 'Yan Shi'a
Asali: Twitter

Dalilinmu na yin Sallar Idi ranar Juma'a bayan yin azumi 28 - 'Yan Shi'a
Sallar Idin mabiya Shi'a
Asali: Twitter

Dalilinmu na yin Sallar Idi ranar Juma'a bayan yin azumi 28 - 'Yan Shi'a
Sallar Idin 'Yan Shi'a
Asali: Twitter

Shugaban ya ce ba su gudanar da Sallar Idi don nuna rashin biyayya ga gwamnati ba, kamar yadda wasu ke zarginsu da aikatawa ba.

DUBA WANNAN: Hotunan yadda El-Rufa'i ya kafa ya tsare a kan iyaka don hana Kanawa shiga Kaduna

A hirar da Sani Funtuwa, wakilin gidan talabijin na Legit.ng Hausa, ya yi da wasu mabiya Shi'a a jihar Bauchi, sun bayyana cewa ana yaudarar 'yan Najeriya tare da siyasantar da batun ganin wata.

Sun kara da cewa sun dauki azuminsu ranar Alhamis bayan ganin jaririn watan Ramadana ranar Laraba, sannan sun Sallace ranar Juma'a bayan ganin jaririn watan Shawwal ranar Alhamis.

Ba a ga sabon watan Shawwal ba a Najeriya, a saboda haka ba za ai Sallah ranar Asabar ba a Najeriya, sai ranar Lahadi, kamar yadda sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya sanar.

Gobe, Asabar, ta ke Sallah a kasar Nijar kamar yadda majalisar malaman kasar ta fitar da sanarwa a yammacin ranar Juma'a bayan ganin wata a wasu garuruwa biyar na kasar.

A cikin sanarwar da malam ta fitar, ta ce an ga jaririn watan Shawwal an garuruwan Maine - Soroa, N'guiguimi da N'Gourti a jihar Diffa mai makwabtaka da jihar Borno.

Majalisar malaman ta sanar da cewa ranar Asabar ce 1 ga watan Shawwal, ranar da jama'a za su yi bikin Sallah bayan sun yi azumi na tsawon kawanki 29.

Tuni Saudiyya ta fitar da sanarwar cewa ba ta ga jaririn watan Shawwal ba, a saboda Sallar Idi sai ranar Lahadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel