Coronavirus: Shugaban kasa ya nemi a bude Masallatai da coci coci a Amurka

Coronavirus: Shugaban kasa ya nemi a bude Masallatai da coci coci a Amurka

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana bukatar dake da akwai na gwamnonin jahohin Amurka su bude Masallatai da coci-coci don sassauta dokar zaman gida.

Gidan Talabijin na Channels ta ruwaito na cewa lokaci yayi da Amurka za ta fara sassauta dokar hana shige da fice da na hana tarukan jama’a saboda annobar Coronavirus.

KU KARANTA: Karamar Sallah: Shugaba Buhari ya bayyana inda zai gudanar da sallar Idin bana

“A yau na tabbata Masallatai da coci coci na daga cikin muhimman wurare da ake gudanar da muhimman ayyuka, ya kamata gwamnoni su bude su domin baiwa jama’a dama gudanar da bauta a karshen makon nan.

“Idan har basu amince suka bude su ba, toh ni zan yi gaban kai nan a bude su, saboda a yanzu a Amurka, muna bukatar addu’a sosai ba kadan ba.” Inji shi.

Coronavirus: Shugaban kasa ya nemi a bude Masallatai da coci coci a Amurka
Donald Trump Hoto: USATODAY
Asali: UGC

A Amurka, gwamnatocin jahohi da na kananan hukumomi sun garkame wuraren ibada saboda rage yaduwar cutar Coronavirus, wanda a yanzu ta kashe fite da mutum 90,000 a Amurka.

A wasu jahohi an samu sassaucin dokar, inda aka bude coci coci amma tare da bayar da tazara, yayin da a wasu jahohi fastoci suka gudanar da wa’azi yayin da mabiya ke cikin motocinsu.

Sai dai a ra’ayinsa, Trump yace a kan me jahohi za su kalli mashayan giya a matsayin wurare masu muhimmanci, kasuwanni, shaguna, gidajen cin abinci, amma su garkame wuraren bauta?

“Wasu gwamnonin suna kallon shagunan sayar da giya a matsayin masu muhimmanci da kuma asibitocin zubar da ciki, amma sun taru sun rufe wuraren bauta, wannan bai kamata ba.” Inji shi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a karamar sallar bana, shi da iyalinsa za su gudanar da sallar Idinsu ne a gida.

Fadar shugaban kasa ce ta bayyana ta bakin kakaakin shugaban kasa Malam Garba Shehu a ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu a babban birnin tarayya Abuja.

Bugu da kari, ba kamar yadda saba shugaban kasa yana karbar baki a lokuttan bukukuwan sallah, a wannan karon shugaban ba zai karbi baki ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel