An ga wata a kasar Nijar, Sarkin Musulmi ya ce ranar Lahadi za ai Sallah a Najeriya

An ga wata a kasar Nijar, Sarkin Musulmi ya ce ranar Lahadi za ai Sallah a Najeriya

- Ba a ga watan Shawwal ba ranar Juma'a a kasar Saudiyya da Najeriya

- Ranar Asabar ta ke Sallah a kasar Nijar kamar yadda majalisar malaman kasar ta fitar da sanarwa a yammacin ranar Juma'a bayan ganin wata a wasu garuruwa biyar na kasar

- Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya sanar da cewa Sallah sai ranar Lahadi a Najeriya

Ba a ga sabon watan Shawwal ba a Najeriya, a saboda haka ba za ai Sallah ranar Asabar ba a Najeriya, sai ranar Lahadi, kamar yadda sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya sanar.

Gobe, Asabar, ta ke Sallah a kasar Nijar kamar yadda majalisar malaman kasar ta fitar da sanarwa a yammacin ranar Juma'a bayan ganin wata a wasu garuruwa biyar na kasar.

A cikin sanarwar da malam ta fitar, ta ce an ga jaririn watan Shawwal an garuruwan Maine - Soroa, N'guiguimi da N'Gourti a jihar Diffa mai makwabtaka da jihar Borno.

An ga wata a kasar Nijar, Sarkin Musulmi ya ce ranar Lahadi za ai Sallah a Najeriya
An ga wata a kasar Nijar
Asali: Twitter

Sauran garuruwan da aka ga watan sun hada da garin Zinder da kuma birnin Magaria na jihar Damagaram da garin Oungoudague a yankin Tsibirin Gobir na gundumar Rounji a Maradin Katsina.

DUBA WANNAN: Hotunan yadda El-Rufa'i ya kafa ya tsare a kan iyaka don hana Kanawa shiga Kaduna

Majalisar malaman ta sanar da cewa ranar Asabar ce 1 ga watan Shawwal, ranar da jama'a za su yi bikin Sallah bayan sun yi azumi na tsawon kawanki 29.

Tuni Saudiyya ta fitar da sanarwar cewa ba ta ga jaririn watan Shawwal ba, a saboda Sallar Idi sai ranar Lahadi.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Saudiyya ta bayar da sanarwar yin Sallar Idi ranar Lahadi a kasar bayan fitar da sanarwar cewa ba su ga watan Shawwal ba a ranar Juma'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel