Yadda hukumar gidan gyaran hali ta Kaduna ta ki karbar fursuna saboda fargabar korona

Yadda hukumar gidan gyaran hali ta Kaduna ta ki karbar fursuna saboda fargabar korona

Hukumar gyaran hali ta jihar Kaduna ta ki karbar wani sabon fursuna da Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC ta kawo mata.

Sanusi Danmusa, shugaban gidan gyaran halin, a ranar Jumaa ya ce an ki karbar sabon fursunan ne saboda kare wadanda ke gidan gyaran halin daga kamu da COVID-19.

Ya ce gidan gyaran halin ta dena karbar sabbin wadanda aka yanke wa hukunci har ma da masu ziyara saboda bullar annobar ta coronavirus.

Fargabar COVID-19: An ki karbar wani da aka kai gidan yari a Kaduna
Fargabar COVID-19: An ki karbar wani da aka kai gidan yari a Kaduna. Hoto daga Sahara reporters
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An kama DPO da sifetan ɗan sanda kan laifin kisan gilla a Legas

An yanke wa Sadiq Musa, mai sanaar canjin kudi hukucin zaman shekaru bakwai a gidan gyaran hali ba tare da zabin biyan tara ba.

Da ya ke tsokaci a kan rashin karbar fursunan, shugaban hukumar EFCC na Kaduna, Yakubu Mailafia ya ce bai san inda hukumar gidan gyran halin ta ke so ya kai wanda aka yanke wa hukuncin ba.

Ya ce, "Hukumar EFCC tana da kaida game da tsare masu laifi kuma gidan gyaran hali shi ne wuri na karshe da ake kai wadanda aka yanke wa hukunci, ina za mu kai su?"

A wani rahoton, kun ji cewa iyalan tsohon shugaban Najeriya, marigayi Umaru Musa Yar’adua sun bayar da gudunmawar kayan abinci da kayan kare kai daga kamuwa da kwayoyin cuta, PPE, ga hukumar kula da Abuja, FCTA.

Sun bayar da kayayyakin ne a matsayin gudunmawarsu wurin yaki da annobar coronavirus da ta adabi kasashen duniya ciki har da Najeriya. An bayar da tallafin ne karkashin gidauniyar iyalin mai suna Women and Youth Empowerment Foundation (WYEF).

Kayayyakin da gidauniyar ta bayar sun hada da takunkumi 1,000, sabulu 1,800, katon din makaroni 100, buhannan semolina 100, buhannan shinkafa 100, hodar wanki leda 23,100 da takunkumin likitoci 13,000.

Yayin mika kayayakin ga FCTA, wakilin iyalan, Malam Abdullahi Umaru Yar’adua, ya yaba da jajircewa da sadaukar da kai da ma'aikatan lafiya ke yi wurin dakile yaduwar cutar.

Mallam Yar’adua ya ce, "Gidauniyar mu ta WYEF da ni kai na muka mika godiyar mu ga gwamnatin tarayyar Najeriya, kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa kan COVID-19, Kwamitin bayar da shawara kan COVID-19 na Abuja da duk wadanda ke aiki don yaki da annobar a kasar."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel