Kasar Saudi Arabia bata ga watan Shawwal ba

Kasar Saudi Arabia bata ga watan Shawwal ba

Gwamnatin kasar Saudi Arabia ta bayyana cewa sai ranar Lahadi za a gudanar da sallar Idin karamar sallah. Ta sanar da hakan ne bayan rashin ganin jinjirin watan Shawwal da aka yi a ranar Juma'a.

Wannan sanarwar na kunshe ne a cikin wata takarda da shafin masallacin Harami na Makka da Madinah ya wallafa a shafinsa na twitter.

"Ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a yammacin ranar Juma'a bayan duban tsanaki," wallafar tace.

Ana fara duba watan Shawwal ne a yayin da watan Azumin Ramadan ya cika 29, a hakan ne wasu lokutan ya ke zarcewa ya kai 30.

Wannan sanarwar na zuwa ne bayan kwanaki biyu da masana ilimin taurari suka tabbatar da cewa ba za a ga watan Shawwal ba a ranar Juma'a.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewawata zai riga rana faduwa a ranar Juma'a, saboda haka sai ranar Lahadi za a yi Idin karamar sallah.

Kasar Saudi Arabia bata ga watan Shawwal ba
Kasar Saudi Arabia bata ga watan Shawwal ba. Hoto daga Haramaininfo
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda miji ya manne al'aurar matarsa da barkono, kasa da yaji kafin ya saka sufa gulu

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel