Yanzu yanzu: Kwamishinan da Ganduje ya tsige ya warke daga cutar korona

Yanzu yanzu: Kwamishinan da Ganduje ya tsige ya warke daga cutar korona

Engineer Muazu Magaji, tsohon kwamishinan Ayyuka na jihar Kano da Gwamna Umar Abdullahi Ganduje ya tsige daga mukaminsa ya warke daga korona kuma an sallame shi.

Injiniya Magaji ne bayyana hakan ne a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Facebook.

A cewarsa, "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah SWT, yau Jumaa 22 ga watan Mayu kuma 29 ga watan Ramadan an tabbatar na warke daga Covid-19 kuma an sallame ni daga cibiyar killacewa."

An tsige Magaji daga mukaminsa ne saboda yin murnar rasuwar tsohon shugaban maaikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

Yanzu yanzu: Kwamishinan da Ganduje ya tsige ya warke daga cutar korona
Yanzu yanzu: Kwamishinan da Ganduje ya tsige ya warke daga cutar korona. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An kama DPO da sifetan ɗan sanda kan laifin kisan gilla a Legas

Gwamna Umar Ganduje, a ranar 18 ga watan Afrilu ne ya sallami Muazu Magaji saboda furta kalamai marasa dadi game da rasuwar Abba Kyari.

Ya kamu da cutar da COVID-19 ne a ranar 7 ga watan Mayu kuma aka tafi da shi cibiyar killacewa da ke jihar Kano domin samun kulawar likitoci.

A wani rahoton, kun ji cewa iyalan tsohon shugaban Najeriya, marigayi Umaru Musa Yar’adua sun bayar da gudunmawar kayan abinci da kayan kare kai daga kamuwa da kwayoyin cuta, PPE, ga hukumar kula da Abuja, FCTA.

Sun bayar da kayayyakin ne a matsayin gudunmawarsu wurin yaki da annobar coronavirus da ta adabi kasashen duniya ciki har da Najeriya. An bayar da tallafin ne karkashin gidauniyar iyalin mai suna Women and Youth Empowerment Foundation (WYEF).

Kayayyakin da gidauniyar ta bayar sun hada da takunkumi 1,000, sabulu 1,800, katon din makaroni 100, buhannan semolina 100, buhannan shinkafa 100, hodar wanki leda 23,100 da takunkumin likitoci 13,000.

Yayin mika kayayakin ga FCTA, wakilin iyalan, Malam Abdullahi Umaru Yar’adua, ya yaba da jajircewa da sadaukar da kai da ma'aikatan lafiya ke yi wurin dakile yaduwar cutar.

Mallam Yar’adua ya ce, "Gidauniyar mu ta WYEF da ni kai na muka mika godiyar mu ga gwamnatin tarayyar Najeriya, kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa kan COVID-19, Kwamitin bayar da shawara kan COVID-19 na Abuja da duk wadanda ke aiki don yaki da annobar a kasar."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel