Covid-19: FG ta yi karin haske kan batun buɗe makarantu a Najeriya

Covid-19: FG ta yi karin haske kan batun buɗe makarantu a Najeriya

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da cewa tana shirin bude makarantu a fadin kasar amma ta ce ba cikin makonni biyu kamar wasu ke hasashe.

Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ne ya yi wannan karin bayanin a ranar Alhamis yayin taron manema labarai a Abuja sakamakon yada jita-jita da mutane ke yi na cewa za a bude makarantu cikin makonni biyu.

Gwamnatin Tarayya ta bada umurnin rufe makarantun ne a dukkan fadin kasar a yunkurin ta na dakile yaduwar annobar coronavirus.

Covid-19: FG ta yi karin haske kan batun buɗe makarantu a Najeriya
Covid-19: FG ta yi karin haske kan batun buɗe makarantu a Najeriya. Hoto daga Ghanamma
Asali: UGC

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai kan ranar bude makarantun, Nwajiuba ya ce za a bude makarantun da zarar an tabbatar dalibai ba za su fuskanci wata barazana ba ga lafiyarsu.

DUBA WANNAN: An kama DPO da sifetan ɗan sanda kan laifin kisan gilla a Legas

Ya ce gwamnati ba za ta aikata duk wani abu da zai jefa rayuwar dalibai cikin hatsari ba da kuma yada cutar da coronavirus a kasar.

Ya kara da cewa ma'aikatar tana aiki tare da sauran hukumomin da abin ya shafa don ganin an tabbatar dalibai ba za su fuskanci wata matsala ba idan an bude makarantun.

Ya ce, "Dukkan mu muna son ganin an bude makarantu kuma za a bude nan ba da dadewa ba. Amma ba zan iya tabbatar muku da cewa nan da makonni biyu za a bude makarantun.

"Kun ji shugaban kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa kan COVID-19, SGF Boss Mustapha, ya ce rufe makarantun lamari ne da ya shafi kasa baki daya.

"A lokacin da kwararru suka tabbatar cewa yaran mu ba za su fuskanci wata matsala ba, za mu bude makarantun. Muna lura da yadda abubuwa ke tafiya kuma muna aiki da hukumomi na gida da kasashen waje.

"Kasashen da ke rubuta jarrabawar (WAEC) suna taro yanzu ma na fito daga taron tare da ministocin Ilimi na kasashen AU, kowa abin ya dame shi. Muna fatar za mu bude makarantu nan ba da dadewa ba.

"A safiyar yau, na yi taro da ma'aikatar Kimiyya da Fasaha. Muna duba yiwuwar gano hanyar da za a yi wa kowanne dalibi feshi kafin ya shiga makaranta da kuma lokacin da zai koma gida.

"Idan mun samar da abinda ya dace a makarantun mu za mu fara budewa. Amma ya zama dole mu tabbatar ba za su kamu da cuta ba ballantana su yada ta a cikin al'umma."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel