Jihohi 35 da aka samu bullar cutar korona yayin da adadin masu cutar ya kai 7, 016 a Najeriya

Jihohi 35 da aka samu bullar cutar korona yayin da adadin masu cutar ya kai 7, 016 a Najeriya

A halin yanzu dai adadin mutanen da aka tabbatar cutar korona ta harba a duk fadin Najeriya sun kai 7, 016 kamar yadda alkaluma suka nuna a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayu.

Najeriya tana daya daga cikin kasashen nahiyar Afirka biyar da cutar korona ta fi tsananta.

Alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC, a ranar Alhamis da daddare sun nuna cewa, an samu karin sabbin mutum 339 da cutar ta harba a jihohi 18 na kasar.

Babu tantanma wannan shi ne adadi mafi girma na sabbin mutanen da aka samu cutar ta harba a rana daya cikin a makon da muka ciki.

Jihar Legas wadda ta kasance babbar cibiyar cutar a Najeriya, ta ci gaba da jan ragama inda ta samu karin sabbin mutum 139, sai kuma jihar Kano da Oyo da suka biyo baya da karin mutum 28 a kowanensu.

Jihar Edo ta biyo baya da karin mutum 25, sai kuma Jihar Katsina 22, Jigawa 14. Jihar Yobe da Filato sun samu karin mutum 13 a kowanensu.

KARANTA KUMA: An nemi Ministan Lantarki ya yi murabus saboda tsige shugaban TCN

Cutar korona ta harbi karin sabbin mutum 11 a birnin Tarayya Abuja, sai kuma jihar Gombe mutum da kuma Ogun inda aka samu mutum 5.

An samu karin mutum 4 a kowane daya daga cikin jihohin Bauchi da Nasarawa. Sai kuma jihar Delta da ta samu karin mutum 3 yayin da jihar Ondo ta samu kari na mutum biyu.

Haka kuma an samu karin mutum 1 a kowane daya daga cikin jihohin Ribas da Adamawa.

Kamar yadda alkaluman NCDC sun nuna, an samu mutum 1,907 da suka warke daga cutar korona a duk fadin kasar kuma tuni aka sallame su daga cibiyoyin killace masu cutar da ke fadin Najeriya.

Da yake komai yana da sababi na faruwarsa, cutar korona ta hallaka mutum 211 a duk fadin kasar.

Har ila yau Kogi da Cross River su ne kadai jihohin da ba a samu bullar cutar ba cikin dukkanin jihohin Najeriya, sai dai ana fargabar cewa rashin daukar matakan da suka dace ya sanya ba a gano masu cutar ba a jihohin biyu.

Ga jerin adadin mutanen da cutar korona ta harba cikin kowace jihar ta cutar ta bulla a fadin kasar kamar yadda alkaluman NCDC suka tabbatar:

1 Lagos: 3093

2 Kano: 875

3 FCT: 446

4 Katsina: 303

5 Borno: 235

6 Bauchi: 228

7 Jigawa: 225

8 Oyo: 190

9 Ogun: 183

10 Kaduna: 170

11 Edo: 144

12 Gombe: 144

13 Sokoto: 113

14 Rivers: 80

15 Zamfara: 76

16 Plateau: 70

17 Kwara: 66

18 Yobe: 45

19 Osun: 42

20 Nasarawa: 38

21 Kebbi: 32

22 Delta: 31

23 Adamawa: 27

24 Niger: 22

25 Ondo: 22

26 Ekiti: 20

27 Akwa: 18

28 Taraba: 18

29 Enugu: 16

30 Ebonyi: 13

31 Abia: 7

32 Bayelsa:

7 33 Imo: 7

34 Anambra: 5

35 Benue: 5

Jimilla: 7016

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel