Allah ya yi wa fitaccen masanin magunguna, Dahiru Wali, rasuwa
Wani sanannen mai hada magani, Dahiru Wali, ya rasu yana da shekaru 85 a duniya.
Wata majiya daga iyalansa mai suna Salahudeen Wali, ya sanar da jaridar Daily Nigerian cewa babban mutumin ya rasu a Kaduna a daren Alhamis.
Kamar yadda yace, za a birne mamacin a garin Kaduna amma a safiyar Juma'a.
A ranar 22 ga watan Yulin 2020, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa sanannen masani a harkar hada magungunan a kan nasarorinsa da gudumawar da yake bada wa a fannin ilimi da lafiya a kasar nan.
Shugaban kasar ya jinjinawa hazakar masanin wanda gogewarsa ta amfani Najeriya.
Ya tabbatar da cewa Wali ya yi amfani da saninsa wajen kafa 'Tsamiya Pharmacy' tun sama da shekaru 50 da suka gabata kuma ana ci gaba da samar da nagartattun magunguna.

Asali: Twitter
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng