An kama DPO da sifetan ɗan sanda kan laifin kisan gilla a Legas

An kama DPO da sifetan ɗan sanda kan laifin kisan gilla a Legas

Rundunar 'Yan sandan jihar Legas ta kama DPO na Ilemba Hausa a karamar hukumar Ojo, CSP Yahaya Adeshina, da Sufeta Charles Okoro a kan kisar mutum biyu – malamin addini da jamiin dan sanda.

An kama Okoro ne saboda harbin wani malamin addini mai shekaru 28, Fatai Oladipupo a Igando da ke Ikotun a Legas.

Okoro yana aiki ne da ofishin yan sanda da ke Ikotun kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Shi kuma Adenshina an kama shi a kan zargin kashe abokin aikinsa, Saja Onalaja Onajide yayin da ya ke kokarin tartwatsa dandazon mutane da suka taru a gaban caji ofis din su.

A kama DPO da dan sanda mai mukamin sufeta kan zargin kisa
A kama DPO da dan sanda mai mukamin sufeta kan zargin kisa. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'An sayar mana da 'yancinmu': Wasu sojoji sun yi Allah-wadai da Buratai

Hakan na cikin wata sanarwa ne mai dauke da saka hannun mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Legas, DSP Bala Elkana, da ya fitar a ranar Alhamis.

Elkana ya ce an kama sufetan ne saboda harbin da aka yi kuma ya yi sanadin kisa a ranar 20 ga watan Mayu.

Ya ce, "An fara gudanar da bincike na cikin gida da aka fi sani da Orderly Room Trial a ofishin 'yan sandan.

"Idan aka same shi da laifi, za a mika shi zuwa sashin masu binciken manyan laifuka da ke Yaba domin a gurfanar da shi a gaban kotu na gama gari.

"A halin yanzu ana cigaba da bincike domin gano abinda ya faru a ranar da aka yi harbin."

Elkana ya ce kwamishinan yan sandan na jihar, Hakeem Odumosu, ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan wadanda suka rasu kuma ya bukaci su kwantar da hankulansu.

Ya kara da cewa, "An dauki wannan matakin ne bayan an shigar da rahoto a wurinsu inda ake zargin DPO na Ilemba Hausa, CSP Yahaya Mohammed Adeshina ya harbe wani saja yayin da ya ke tarwatsa mutane a gaban caji ofis.

"An kama DPO kuma ana tsare shi a ofishin CID. An karbe bindigar shi domin a gudanar da bincike. Rundunar ta umurci a bincika gawar mamacin don gano abinda ya kashe shi."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel