An nemi Ministan Lantarki ya yi murabus saboda tsige shugaban TCN

An nemi Ministan Lantarki ya yi murabus saboda tsige shugaban TCN

Kungiyar Ma'aikatan Wutar Lantarki ta Kasa (NUEE) ta yi kira ga Ministan Wutar, Ministan Wutar Lantarki, Mamman Saleh, da ya gaggauta yin murabus daga mukaminsa.

Kungiyar NUEE ta yi wannan kira kan abin da ta ce Ministan yana da rashin cikakken ilimi na ma’aikatar da yake kulawa da ita.

Wannan kira ya zo ne biyo bayan tsige shugaban kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN), Mista Usman Muhammad, da Gwamnatin Tarayya ta yi a ranar Talata, 19 ga watan Mayu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata, ta bakin Ministan Wutar Lantarki, ya sallami Manajan Darakta na TCN kuma ya maye gurbinsa da Injiniya Sule Ahmed Abdulaziz, a matsayin mai rikon kwarya.

Cikin sanarwar da fito daga ofishin Ministan wadda take dauke da sa hannun mai magana da yawun Ma'aikatar Lantarki, Aaron Artimas, ba tare da bayar da takamaiman dalili ba, ta sauke Injiniya Muhammad daga mukaminsa.

Sai dai sanarwar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito ta bayyana cewa, sallamar Injiniya Muhammad na daya daga cikin sauye-sauyen fasali da yi wa kamfanin TCN saitin da aka kudirta.

Hakan dai bai yiwa ma'aikatan Wutar Lantarkin dadi ba, inda a yanzu suke kiran Ministan da ya gaggauta yin murabus.

Ma'aikatan Lantarkin cikin wata sanarwa da sa hannun babban sakataren kungiyarsu, Joe Ajaro, ta kalubalanci Ministan da ya fito a yi gaba-da-gaba da shi a daya daga cikin manyan gidajen Talbijin na kasa.

Ministan Lantarki; Saleh Mamman
Ministan Lantarki; Saleh Mamman
Source: Facebook

Kungiyar ta ce Ministan ya bayyana a daya daga cikin manyan gidajen Talbijin na kasa domin ya tafka muhawara da al'umma a kan yadda za a magance matsalolin Wutar Lantarki da ake fuskanta a kasar.

Ta ce "tana son ta gano ko an tsige shugaban TCN ne a kan rashin kwazon aiki ko kuma rashawa, amma ba dai don rashen hangen nesa ko kuma karfin ikon kowane minista ba."

KARANTA KUMA: An ci gaba da musayar yawu tsakanin Amurka da China kan sakacin bullar annobar korona

A yayin da wannan lamari bai yi wa Kungiyar NUEE dadi ba, Kungiyar manyan Ma'aikatan Wutar Lantarki, SSAEAC, sun bayyan farin cikin kan hukuncin da Buhari da Ministansa suka zartar.

SSAEAC ta ce tsige shugaban TCN ya yi daidai domin kuwa tun da ma can bai cancanci rike mukamin ba.

A sanarwar da SSAEAC ta fitar mai lamba SSAEAC/NHQ/SEC.05/057/2020, ta yi zargin cewa, tsohon shugaban na TCN ya rika cin amanar kujerarsa ba tare da an yi masa hukunci ba.

Ta ce ya yiwa kamfanin TCN asarar sama da Naira biliyan 30 a tsawon shekaru ukun da suka gabata.

Kwanaki uku da suka gabata ne kungiyar SSAEAC ta fara barazanar tafiya wani sabon yajin aiki saboda abin da ta kira sabawa doka kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

‘Yan kungiyar SSAEAC sun bayyana tsige shugabansu, Dr. Chris Okonkwo, da aka yi a matsayin saba doka, don haka sun fara huro wutar shiga wani danyen yajin aiki.

A ranar 24 ga watan Afrilun 2020 ne Injiniya Muhammad ya sallami jagoran kungiyar SSAEAC Dr. Okonkwo daga aiki. A yanzu dai an yi 'ba wan ba kanin'.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel