COVID-19: An soke hawan Sallah a Zazzau

COVID-19: An soke hawan Sallah a Zazzau

Majalisar masarautar Zazzau a jihar Kaduna a ranar Alhamis sanar cewa bana ba za ta yi bikin hawan Sallah kamar yadda aka saba yi a duk shekara ba, bayan kamalla azumin Ramadan.

Alhaji Umaru Shehu Idris, Dan Isan Zazzaun kuma mataimakin sakataren masarautar Zazzau ne bayar da sanarwar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi kira da mazauna garin su kasance masu biyayya ga doka da oda.

Ya ce kamar yadda gwamnatin tarayya da na jihohi suka bayar, masarautar ta soke hawan sallar ne domin guje taron alumma masu zuwa kallo daga jihar, wasu jihohin da ma kasashen ketare.

COVID-19: An soke hawan Sallah a Zazzau
COVID-19: An soke hawan Sallah a Zazzau. Hoto daga Arewa Heritage
Source: UGC

DUBA WANNAN: Sojoji sunyi ruwan bama–bamai a sansanin 'yan Boko Haram a kusa da Sambisa

Alhaji Umar Idris ya kara da cewa, "Muna kira ga alumma su yi hakuri da wannan matakin da muka dauka.

"An dauki matakin ne domin kare mu.

"Kowa ya san hadarin da COVID-19 ke da shi ga rayuwamu.

"Saboda haka, mutane su dauki wannan lamarin a matsayin kaddara.

"Addinin mu ya koyar da mu yarda da kaddara mai dadi da mara dadi.

"Saboda hakan ne masarautar Zazzau ta soke dukkan hawan salla da sauran shagulgula ne karamar sallah.

"Babu wata tawaga ko mutum da zai hau doki.

"Dukkanmu mu zauna a gida muyi amfani da wannan damar muyi addua Allah ya kawar da annobar.

"Muna son yin amfani da wannan damar mu yi wa mutane fatan yin bikin sallah lafiya da fatan Allah ya amsa ibadun mu."

Masarautar ta kuma shawarci mutane su cigaba da kiyayye kansu daga kamuwa da COVID-19 ta hanyar bin shawarwarin hukumomin da abin ya shafa.

Baya ga masarautar Zazzau, an dakatar da shagulgulan Sallah a wurare da dama a arewacin Nigeria saboda yadda ake fargabar yaduwar cutar korona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel