'Yan gida daya su 10 sun kamu da korona a Kaduna

'Yan gida daya su 10 sun kamu da korona a Kaduna

Mutane 10 dukkansu yan gida daya sun kamu da muguwar kwayar cutar coronavirus a jihar Kaduna.

Gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufai ne ya bayyana hakan yayin da ya ke zantawa da manema labarai.

Ya ce an samu karin mutum 18 da suka kamu da cutar a jihar a ranar 21 ga watan Mayu. 14 daga cikinsu sun fito ne daga karamar hukumar Kaduna ta Arewa, biyu daga Zaria.

Sauran kuma guda 1,1 daga kananan hukumomin Chikun da Sabon Gari.

Ga dai yadda rubuta a shafin Twitter na gwamnatin jihar Kaduna @GovKaduna.

"Bayani kan Covid-19: An samu sabbin mutum 18 da suka kamu, 10 daga ciknsu yan gida daya ne. 14 daga cikin sabbin kamun daga karamar hukumar Kaduna ta Arewa suka fito, biyu daga Zaria sai 1,1 daga kananan hukumomin Chikun da Sabon Gari."

DUBA WANNAN: COVID-19: Gwamnonin Arewa sun nemi tallafin kudi wurin Buhari

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce shi da kansa zai fita domin tsare iyakokin Kaduna da jihar Kano a ranar Sallah domin tabbatar da cewa babu wani da ya shigo jiharsa daga Kano a yunkurinsa na dakile yaduwar cutar.

Ana sa ran za a gudanar da bikin sallar na wannan shekarar a ranar Asabar ko Lahadi ne idan azumin watan Ramadan ya zo karshe.

Tuni dai gwamnatin jihar Kaduna ta sassauta dokar kulle inda ta ware wa mutane kwanaki biyu don su fita su siya kayayyakin da suke bukatar a ranakun Laraba da Alhamis don tabbatar da kowa ya zauna a gida a karshen makon.

El Rufai ya yi wannan gargadin ne a yayin hira da aka yi da shi a wasu gidajen rediyo a ranar Talata inda ya ce; "Da kai na zan fita in rika zaga iyakokin Kaduna da Kano kuma ba zan bar wurin ba sai dare don in ga wanda zai shigo Kaduna. Ba zan bar wurin ba sai dare."

Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda mutane ke shiga da fita jihar duk da umurnin shugaban kasa na hana zirga zirga tsakanin jihohi, inda ya ce galibin wadanda suke dauke da cutar a jihar sunyi tafiya.

Ya jingina laifi a kan wasu jamian tsaro marasa kishin kasa da ke karbar cin hanci a hannun matafiya su barsu su shigo jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

El Rufai ya ce, "Ba abinda ba mu yi ba amma jamian tsaro ba su bamu hadin kai. Mun samu labarin yadda wasu direbobin motocin haya da wasu ke biyansu kudi don su shigo Kaduna."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel