'An sayar mana da 'yancinmu': Wasu sojoji sun yi Allah-wadai da Buratai

'An sayar mana da 'yancinmu': Wasu sojoji sun yi Allah-wadai da Buratai

– Wasu jamian sojoji da ke aikin yaki da taadanci a jihar Yobe sunyi Allah wadai da Laftanar Janar Buratai

– Sojojin da aka ji muryarsu cikin wani faifan bidiyo da suka dauka sun koka kan irin yanayin da suke ciki a fagen famar bayan wani hari da yan taadda suka kai musu

– Rundunar sojojin ta Najeriya ta ce za a duba kwakwalen sojojin da suka dauki wannan bidiyon da ake ce sunyi ne sakamakon rudewa da rikicewar kwakwalwa

Rundunar sojojin Najeriya ta ce za a binciki kwakwalen wasu sojojinta da suka yi wani bidiyo suna Allah wadai ga shugabancin rundunar da ke jagorantar yakin da suke yi da yan taadda a yankin Arewa maso Gabas.

Sanarwar ta hedkwatar tsaro ta Najeriya ta fitar a ranar Alhamis ta ce an yi wa jamianta na rundunar Kantana Jimlan da ke Buni Yadi - Buni Gari da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe kwantan bauna a ranar 18 ga watan Mayu.

An sayar mana da 'yancinmu - Bidiyon sojoji su na allawadai da Buratai
An sayar mana da 'yancinmu - Bidiyon sojoji su na allawadai da Buratai. Hoto daga Premium Times
Source: UGC

DUBA WANNAN: Zamfara: Matawalle ya bayyana yadda zai 'yi maganin' 'yan bindiga

Sanarwar ta ce sojoji biyu sun kwanta dama yayinda wasu uku sun samu rauni sakamakon taka nakiya da suka yi.

Wata babban tankar yaki da babbar motar da ke dauke da ruwan da sojojin ke amfani da shi sun kone yayin harin.

Sanarwar ta kara da cewa sojojin sun kuma kashe yan taadan kungiyar Boko Haram uku sannan wasu adadi masu yawa da ba a tabbatar ba sun tsere da raunika a jikinsu.

Sakamakon rudewa da rikicewar kwakwalwar wasu sojoji biyu da suka tsira daga harin suka dauki bidiyo inda suke Allah-wadai da rundunar sojin da kuma Hafsan sojin kasa Laftanar Janar Yusuf Buratai.

A bidiyon da ya bazu a dandalin sada zumunta, an ji muryar wasu sojoji suna cewa, "yadda ake kula da mu bai kamata ba, an sayar mana da 'yancinmu. Burutai, wannan ba alheri ba ne a wajen ka, ku duba yadda suka yi mana kofar rago".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel