Yadda miji ya manne al'aurar matarsa da barkono, kasa da yaji kafin ya saka sufa gulu

Yadda miji ya manne al'aurar matarsa da barkono, kasa da yaji kafin ya saka sufa gulu

Wani magidanci mai shekaru 30 a duniya wanda ya rufe al'aurar matarsa da sufa gulu ya shiga hannun jami'an tsaro bayan kwanaki kadan da aka bazama nemansa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wani mutum mai suna Kifo Muriuki wanda ya zargi matarsa da bibiyar wasu mazan ya yaudareta zuwa rafin Kathita.

A nan yayi barazanar halaka ta matukar bata amince da umarninsa ba. Ya hada yaji, gishiri da albasa sannan ya saka a gabanta bayan yayi amfani da wuka mai kaifi. Daga nan sai ya saka sufa gulu da kasa ya manne gaban matarsa.

An fara neman wanda ake zargin tun ranar Asabar 16 ga watan Mayu a lokacin da ya aikata mugun aiki. Daga bisani an kama shi a yankin Kaningo da ke Kitui bayan tsananta nemansa da aka yi.

Kamar yadda sashen binciken manyan laifuka na kasar Kenya ya wallafa a shafinsa na twitter: "James Kifo Muruiki mai shekaru 30 a duniya ya shiga hannun jami'an tsaro bayan zarginsa da ake da yunkurin halaka matarsa.

"An kama shi a maboyarsa da ke yankin Kaningo da ke Kitui bayan tsananta nemansa da aka yi."

Yadda miji ya manne al'aurar matarsa da sufa gulu
Yadda miji ya manne al'aurar matarsa da sufa gulu. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dakarun sojin Najeriyasun tarwatsa ma'adanar makaman 'yan ta'adda a Borno, sun bi ta wani da motar yaki (Bidiyo)

A wani labari na daban, a ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a sake tura tawagar kwararru jihar Kogi don tabbatar da cewa an samar da abubuwan da jihar ke bukata wajen yaki da cutar coronavirus.

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya bada wannan sanarwan a Abuja ga taron manema labarai yayin da suke tattaunawa da kwamitin yaki da cutar coronavirus na fadar shugaban kasa.

Idan za mu tuna, gwamnatin jihar ta hana NCDC bincike ko tallafa mata wajen shirya wa cutar coronavirus a yayin da suka ziyarci jihar.

Wannan zargin ya kawo rashin jituwa tsakanin jami'an NCDC din da jihar Kogi inda jami'an suka bar jihar ba tare da bin dokar gwamna Yahaya Bello ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel