COVID-19: Iyalan marigayi Yar’adua sun bayar da tallafin korona

COVID-19: Iyalan marigayi Yar’adua sun bayar da tallafin korona

Iyalan tsohon shugaban Najeriya, marigayi Umaru Musa Yar’adua sun bayar da gudunmawar kayan abinci da kayan kare kai daga kamuwa da kwayoyin cuta, PPE, ga hukumar kula da Abuja, FCTA.

Sun bayar da kayayyakin ne a matsayin gudunmawarsu wurin yaki da annobar coronavirus da ta adabi kasashen duniya ciki har da Najeriya.

An bayar da tallafin ne karkashin gidauniyar iyalin mai suna Women and Youth Empowerment Foundation (WYEF).

COVID-19: Iyalan marigayi shugaban kasa Yar’adua sun bayar da tallafin korona
COVID-19: Iyalan marigayi shugaban kasa Yar’adua sun bayar da tallafin korona
Source: UGC

Kayayyakin da gidauniyar ta bayar sun hada da takunkumi 1,000, sabulu 1,800, katon din makaroni 100, buhannan semolina 100, buhannan shinkafa 100, hodar wanki leda 23,100 da takunkumin likitoci 13,000.

DUBA WANNAN: Zamfara: Matawalle ya bayyana yadda zai 'yi maganin' 'yan bindiga

Yayin mika kayayakin ga FCTA, wakilin iyalan, Malam Abdullahi Umaru Yar’adua, ya yaba da jajircewa da sadaukar da kai da ma'aikatan lafiya ke yi wurin dakile yaduwar cutar.

Mallam Yar’adua ya ce, "Gidauniyar mu ta WYEF da ni kai na muka mika godiyar mu ga gwamnatin tarayyar Najeriya, kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa kan COVID-19, Kwamitin bayar da shawara kan COVID-19 na Abuja da duk wadanda ke aiki don yaki da annobar a kasar."

Da ta ke karbar kayan tallafin, karamar ministan Abuja, Dr Ramatu Tijjani Aliyu da yabawa iyalan na Yar’adua bisa wannan karamci da suka yi da ta ce abin koyi ne ga wasu manyan iyalai a kasar.

Dr Aliyu ta ce, "Mun yi farin cikin samun tallafi daga iyalan tsohon shugaban kasar mu da suka samu wakilcin yayansu uku. Wannan tallafin zai taimaka sosai wurin rage radadin annobar COVID-19 ga mazauna Abuja da sauran yan Najeriya."

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar masarautar Zazzau a jihar Kaduna a ranar Alhamis sanar cewa bana ba za ta yi bikin hawan Sallah kamar yadda aka saba yi a duk shekara ba, bayan kamalla azumin Ramadan.

Alhaji Umaru Shehu Idris, Dan Isan Zazzaun kuma mataimakin sakataren masarautar Zazzau ne bayar da sanarwar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi kira da mazauna garin su kasance masu biyayya ga doka da oda.

Ya ce kamar yadda gwamnatin tarayya da na jihohi suka bayar, masarautar ta soke hawan sallar ne domin guje taron alumma masu zuwa kallo daga jihar, wasu jihohin da ma kasashen ketare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel