Labari mai dadi: WHO ta nuna goyon baya a kan maganin cutar korona na kasar Madagascar

Labari mai dadi: WHO ta nuna goyon baya a kan maganin cutar korona na kasar Madagascar

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta bayyana cewa ta fara duba yiwuwar la'akari da maganin gargajiya na kasar Madagascar, wanda ake ikirarin yana maganin cutar korona.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, Hukumar ta ce akwai yiwuwar za ta fara aiki a kan maganin na Madagascar wajen nema masa samun tabbacin ilimin kimiya ko kuma sabanin haka.

Shugaban Madagascar, Andry Rajoelina, shi ne ya sanar da hakan cikin wani sako da ya wallafa a kan shafinsa na Twitter a ranar Laraba.

Rajoelina ya sanar da hakan ne bayan wata muhimmiyar ganawa da ya yi tare da Darakta Janar na WHO, Tedros Ghebreyesus.

Ya ce WHO bayan taya kasarsa murnar samar da wannan magani da ake kira COVID Organics, ta kuma ce za ta fara nema masa tabbacin ilimin kimiya ta hanyar gwaji a nahiyyar Afirka.

Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar Lafiya ta Duniya ta nemi ba wa kasar Madagascar cin hancin Dala miliyan 20 domin ta gurbata maganin na COVID Organics da aka samar.

Shugaban na Madagascar a karshen makon da ya gabata, shi ne ya yi furucin wannan tuggu da WHO take kokarin shukawa saboda neman ta cimma wata manufa.

Shugaban Madagascar, Andry Rajoelina yana kwankwadar maganin COVID Organics
Shugaban Madagascar, Andry Rajoelina yana kwankwadar maganin COVID Organics
Asali: Facebook

Ya kuma bayyana cewa, ba wani dalili bane ya sanya sauran kasashen duniya suka ki karba tare da ba wa maganin COVID Organics muhimmanci face kawai don an samar da shi ne a nahiyyar Afirka.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta nemi Shugaba Buhari ya daukewa magungunan zazzabin cizon sauro biyan haraji

Dama tun a baya Hukumar Lafiya ta Duniya, tana nan a kan bakanta na cewa kawo yanzu ba a samu wani maganin cutar korona ba, saboda haka mutane su daina amfani da maganin da ba shi da tabbas.

Hakan ya sanya a baya, WHO ta yi watsi da ikirarin da shugaban Madagascar ya yi na cewa maganin gargajiya da aka samar a kasarsa na warkar da masu cutar korona.

Kasar Madagascar dai wani tsibiri ne a tsakiyar tekun Indiya da ke da nisan kilomita 400 daga gabashin Afirka, al’ummar kasar sun kai miliyan 26 tun kidayar da aka gudanar a shekarar 2018.

Madagascar ta binciko wannan magani na gargajiya daga wani ganye wanda ta sarrafa shi kamar ganyen shayi. Kuma cibiyar bincike ta kasar ita ce ta binciko maganin.

A zahiri dai maganin yana dauke da sunadarin Artemisia, wanda akasari ake amfani da shi don maganin zazzabin cizon sauro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel