Majalisar Dattawa ta nemi Shugaba Buhari ya daukewa magungunan zazzabin cizon sauro biyan haraji

Majalisar Dattawa ta nemi Shugaba Buhari ya daukewa magungunan zazzabin cizon sauro biyan haraji

Majalisar Dattawa tana rokon Gwamnatin Tarayya ta fadada dokar dauke nauyin haraji na shigo da wasu magunguna masu muhimmanci kamar na zazzabin cizon sauro.

Wannan yana daya daga cikin tattaunawar da majalisar dattawan Najeriya ta yi yayin zaman da ta gudanar a ranar Talata, 19 ga watan Mayu, 2020.

Majalisar ta kuma nemi a dauke harajin shigo da kayayyaki da ake kira VAT a kan magungunan ciwon suga, hawan jini, cutar daji da sauran magungunan da kananan yara da tsofaffi ke da bukata.

Shugabannin majalisar sun kudiri aniyar hakan ne da manufar tausayawa kananan yara masu rauni da kuma tsofaffi wadanda mahukuntan lafiya suka tabbatar sun fi hatsarin kamuwa da cutar korona.

Haka kuma majalisar kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito, ta nemi shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da shirin tsawwala kudin wuta duba da radadin da annobar korona ta jefa al'umma ciki.

Shugaban Majalisar Dattawa; Sanata Ahmed Lawan
Shugaban Majalisar Dattawa; Sanata Ahmed Lawan
Source: UGC

A yayin haka kuma, Majalisar ta nemi Gwamnatin Tarayya ta sake yin dogon nazari a kan cefanar da akalar rarraba wutar lantarki da ta yi ga 'yan kasuwa masu zaman kansu.

Majalisar ta ce hasken lantarki ba zai wadata ba a Najeriya har zuwa wani lokaci mai tsawo muddin ba a sake wani dogon waiwaye ba a kan al'amuran gudunarwa na kamfanonin rarraba wutar lantarki tare da sauya musu fasali.

KARANTA KUMA: Kishi: An gutsure kunnen wata mata a Jigawa

A jawabin da ministar kudin Najeriya Zainab Ahmed ta yi makonni da suka gabata, ta ce Gwamnatin Tarayya ta shirya ba da tallafi ga bangaren kiwon lafiya ta hanyar cire haraji kan kayayyakin maganin da ake shigowa da su kasar.

Furucin ministar ya zo ne bayan tattaunawa da shugabannin majalisar dattawa da kuma gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, kan rage burikan kasafin kudin kasar na bana.

A Larabar da ta gabata ne majalisar zartarwa ta amincewa ma'aikatar ilimi da ma'aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, su kashe N1,348,057,600 wajen aiwatar da wasu muhimman ayyuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel