Sojoji sunyi ruwan bama–bamai a sansanin 'yan Boko Haram a kusa da Sambisa

Sojoji sunyi ruwan bama–bamai a sansanin 'yan Boko Haram a kusa da Sambisa

Hedkwatan Tsaro ta Najeriya ta ce sojojin saman ta na Operation Lafiya Dole, OPLD, a ranar Litinin sun lalata cibiyar tsara zirga–zirga ta kungiyar Boko Haram/ISWAP da ke Njimia kusa da dajin Sambisa.

Shugaban sashin watsa labarai na hedkwatan tsaron, Manjo Janar John Enenche ne ya sanar da hakan a ranar Talata a Abuja.

Mr Enenche ya ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayannan sirri da kuma amfani da naurar leken asiri ta ISR wurin tabbatar da yan taadan na wurin kafin kai harin.

Ya kara da cewa sojojin sun gano wasu kananan gidaje da ke kusa da sansanin da yan ta'adan ke amfani da su wurin ajiye man fetur da wasu kayayyakin bukatunsu.

NAF ta yi ruwan bama–bamai a sansanin 'yan Boko Haram a kusa da Sambisa
NAF ta yi ruwan bama–bamai a sansanin 'yan Boko Haram a kusa da Sambisa. Hoto daga The Nation
Source: UGC

DUBA WANNAN: Boko Haram: Sojojin Najeriya sun kashe dandazon 'yan ta'adda a Yobe

A cewarsa, sojojin saman sunyi amfani da jiragen yaki wurin lalata sansanin da yan ta'adan da ke ciki.

"Sojojin saman Najeriya, (NAF) sun kai hari inda suka lalata rumbun ajiyar kayan yan ta'adan Boko Haram tare da lalata wasu gine ginen da yan ta'addan ke amfani da su a wurin.

"Shugaban hafsin sojojin saman Najeriya ya yabawa sojojin kan jajircewarsu da kwarewa wurin aiki inda ya bukaci su cigaba da gudanar da aikinsu na kawo karshen ta'adanci a Arewa maso Gabas," in ji shi.

Har wa yau, Mr Enenche ya kuma bayyana cewa sojojin Combat Team 1, na Operation Kantana Jimlan da ke sintiri a Buni Yadi – Buni Gari sunyi taka nakiya kuma sunyi arangama da 'yan Boko Haram a ranar Lahadi.

Ya ce yan ta'adan sun yi wa sojojin kwantar bauna ne a Buni-Gari a karamar hukumar Gujba da ke jihar Yobe inda sojoji biyu suka kwanta dama yayin da nakiyar ta ya tayi wa sojoji uku rauni.

A cewarsa, babban motar sojoji da ke dauke da ruwa da wacce ke dauke da sojoji duk sun lalace sakamakon nakiyar da suka taka.

Ya ce, "An kashe yan ta'adda uku yayinda wasu dama sun tsere da rauni a jikinsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel