Covid-19: Likitoci 8 sun kamu da korona a Zamfara

Covid-19: Likitoci 8 sun kamu da korona a Zamfara

Kungiyar Likitoci ta Najeriya, NMA, reshen jihar Zamfara ta sanar da cewa an tabbatar da cewa likitoci takwas sun kamu da coronavirus.

Mataimakin shugaban na NMA, Dr Mannir Bature ya shaidawa manema labarai a ranar Laraba cewa, "Cikin mutum 80 da suka kamu a jihar, kashi 10 cikin 100 likitoci ne da suka yi cudanya da majinyata.

"Muna farin cikin sanar da cewa cikin wadanda suka kamu, kashi 60 cikin 100 sun warke an sallame su yayinda sauran suna samun sauki," in ji shi.

Covid-19: Likitoci 8 sun kamu da korona a Zamfara
Covid-19: Likitoci 8 sun kamu da korona a Zamfara. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

Dr Bature ya kuma ce wasu likitoci 30 da suka yi cudanya da abokan aikinsu da suka kamu da cutar ta korona sun killace kansu domin kare yaduwar cutar a jihar.

DUBA WANNAN: Boko Haram: Sojojin Najeriya sun kashe dandazon 'yan ta'adda a Yobe

"Wannan halin da muka shiga ya kawo cikas ga ayyukan likitoci a jiha musamman a yanzu da muke fama da annoba saboda dukkan jihar likitoci 3000 muke da su har da wadanda ke aiki a asibiti masu zaman kansu.

"Wannan na daga cikin dalilin da yasa kungiyar ke shawartar gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle ta karo likitoci da sauran maaikatan lafiya tare da horas da dalibai a jihar su karanci aikin likitoci," in ji shi.

A wani labari na daban, gwamnatin Jihar Kwara ta yi rashin wakilin ta da Shugaba Buhari ya zaba domin nada shi mamba a Hukumar Daidaito a Ayyukan Gwamnatin Tarayya (FCC), James Kolo.

Marigayi Kolo ya rasu ne a ranar Talata a Asibitin Koyarwa ta Jamiar Ilorin (UITH) bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Dan asalin garin Patigi ne a karamar hukumar Patigi na jihar.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar ta mika sakon taaziyarsa da mutanen garin Patigi da yayan All Progressives Congress (APC) game da rasuwar dan siyasan.

AbdulRazaq, a cikin sanarwar da hadiminsa Rafiu Ajakaye ya fitar ya bayyana Patigi a matsayin mutum mai yi wa jamiyya biyayya kuma mai kaunar aiki tare da mutane wadda rasuwarsa babban rashi ne ga iyalansa, mutanen karamar hukumar Patigi da jihar baki daya.

Gwamnan ya ce, "Munyi bakin cikin rasuwar Mr Kolo da ya mutu bayan rashin lafiya. Mutum ne mai kaunar jamiyya kuma mai sada zumunci da ya yi aiki tukuru tare da wasu masu kishin jam'iyya domin ganin APC ta yi nasara a jihar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel