Kishi: An gutsure kunnen wata mata a Jigawa
Zafin kishi ya sa wata mata ta gutsure kunnen abokiyar zamanta da hakori yayin da suka ba wa hammata iska jihar a Jigawa da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Fada ya kaure a tsakanin kishiyoyin biyu saboda wata sa'insa da 'dan daya daga cikinsu ya haddasa kamar yadda jaridar Aminiya ta wallafa.
Wannan mummunan lamari ya auku ne a tsakanin matan wani mutum da a ke kira Dan Borno, masu suna Zubaida da Rabi, a cikin gidan mijin nasu da ke Unguwar Zai a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa.
'Dan karamin yaƙi ya kaure tsakanin Zubaida da Rabi inda suka yi ta musayar yi wa juna bugun dawa bayan da 'dan Rabi ya zuba ruwa a cikin tankin injin Zubaida saboda ta zage shi.
Ana tsaka da wannan mummunan ruguntsumi ne Zubaida ta samu nasarar kafta wa Rabi cizo a kunne, har sai da kai ta gutsure rabin kunne.

Asali: Twitter
Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Jigawa, SP Audu Jinjiri, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari da cewa kishiyoyin sun amsa tambayoyi gabani a bayar da belinsu a ofishin 'yan sanda na karamar hukumar Dutse.
KARANTA KUMA: Majalisar zartarwa ta amince da ayyukan N1.33bn a jami'ar Filato da Hukumar Kwastam
Yayin ci gaba da ba da tabbaci a kan lamarin, SP Jinjiri ya ce za a gurfanar da matan biyu a gaban kuliya inda kowacce za ta fuskanci hukunci daidai da abinda suka aikata.
Wani makwabcin Dan Borno ya ba da shaidar yadda zafin kishi ya sanya a ka dade ana zaman doya da manja a tsakanin Matan biyu musamman a kan 'ya'ya, har ta kai babu damar 'ya'yan daya su kai ziyara ko da kofar dakin daya.
Babu shakka zafin kishi ya kan sa mata musamman a Arewa su aikata laifin da za su yi da na saninsa har tsawon rayuwa. Sai dai kuma irin haka tana kasancewa har ta a kan mazaje yayin da a ka samu kuskure na zaman aure.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng