Dandazon masu bin gwamnati bashin kudi sun hana Sabo Nanono shiga ofis a Abuja

Dandazon masu bin gwamnati bashin kudi sun hana Sabo Nanono shiga ofis a Abuja

Wasu yan kwangila da suka yi ma ma’aikatar noma da raya karkara aiki sun yi ma ma’aikatar tsinke a ranar Laraba, inda suka yi bore tare da hana minista Sabo Nanono shiga ofis.

Yan kwangilar sun nuna bacin ransu dangane da yadda ma’aikatar ke jan kafa wajen biyansu kudaden su bayan sun kammala aikin da aka basu, don haka suka nemi a basu kudinsu.

KU KARANTA: Yaki da yan bindiga: Dakarun hadaka sun isa jahar Katsina don gudanar da aiki na musamman

A yayin wannan hayaniya ne mutanen suka yi bake bake a gaban ofishin ministan, kuma duk kokarin da jami’an ma’aikatan suka yi na tausansu ya ci tura, inda suka tubure sai an biya su.

An jiyo su suna wakar: “A sallami Nanono; A sallami babban sakatare; a biya mu kudin mu.” Suka dage kai da fata ba za su tafi ba sai minista Nanono ko babban sakatare ya yi musu jawabi.

Mutanen sun yi korafin cewa yanzu haka akwai abokan su da suka mutu sakamakon bakin cikin danne hakkokinsu da gwamnati ta yi, inji rahoton jaridar Punch.

Dandazon masu bin gwamnati bashin kudi sun hana Saba Nanono shiga ofis a Abuja
Sabo Nanono
Source: Twitter

Wani daga cikinsu mai suna Lucky yace: “Tun shekarar 2018 aka bamu kwangila, kuma mun zartar da kwangilar kamar yadda aka bukata, har ma ma’aikatar ta bamu shaidar kammala aiki, kullum da shi muke zuwa nan wajen don a biya mu kudinmu, amma shiru kake ji.

“Daga baya ma’aikatar ta ware wasu zababbun yan kwangila ta biya su kudinsu, bamu san dalilinsu ba, mun tattauna da minista da babban sakataren ma’aikatar, amma babu wani labari.” Inji shi.

Duk kokarin jin ta bakin ma’aikatar ya ci tura, saboda kakaakin ma’aikatar, Theodore Ogaziechi baya daukan kiran da aka masa, kuma ya amsa sakon kar ta kwana da aka tura masa ba.

A wani labari kuma, saboda rashin kudaden shiga a hukuma kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya, FAAN, FAAN ta ce ba lallai bane ta iya biyan cikakken albashin ma’aikatanta.

Hukumar ta bayyana cewa ma’aikata za su fuskanci canji a albashinsu daga watan Mayu, amma da zarar jirage sun cigaba da tashi za ta cigaba da biyansu cikakkun hakkokinsu.

Hukumar FAAN ta shiga matsalar albashi ne tun bayan da aka dakatar da sauka da tashin jirage a Najeriya a wani mataki na dakile yaduwar cutar Coronavirus tun a watan Afrilu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel