COVID-19: Gwamnonin Arewa sun nemi tallafin kudi wurin Buhari

COVID-19: Gwamnonin Arewa sun nemi tallafin kudi wurin Buhari

Kungiyar Gwamnonin Arewa ta bukaci gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta samar mata da kudade na musamman don yaki da annobar COVID-19 a yakin.

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da ba wa gwamnatin Legas Naira biliyan 10 don yaki da annobar.

A jawabin bayan taro da kungiyar gwamnonin arewan ta fitar a ranar Laraba, gwamnonin sun ce johohinsu ne ke da kashi 54 cikin 100 na wadanda suka kamu saboda haka suke neman tallafin.

COVID-19: Gwamnonin Arewa sun nemi tallafin kudi wurin Buhari
COVID-19: Gwamnonin Arewa sun nemi tallafin kudi wurin Buhari. Hoto daga Guardian
Source: UGC

DUBA WANNAN: Boko Haram: Sojojin Najeriya sun kashe dandazon 'yan ta'adda a Yobe

Simon Lalong, gwamnan jihar Plateau kuma shugaban kungiyar ne ya jagoranci taron da gwamnonin suka yi ta intanet kamar yadda Sahara reporters ta ruwaito.

Gwamnonin sun kuma ce har yanzu suna kan bakarsu ta siyan motocin da za su rika yawo musamman a karkara suna yi wa mutane gwajin kwayar cutar da COVID-19.

A kan batun rufe iyakokin jihohi, gwamnonin sun nuna bacin ransu kan yadda har yanzu mutane ke ketarawa zuwa jihohi duk da dokoki da aka saka a jihohi har ma da gwamnatin tarayya.

"Kungiyar ta ce za ta cigaba da kira ga Gwamnatin Tarayya ta tallafa mata wurin yaki da annobar coronavirus duba da cewa yankin ne ke da kashi 54 a kasar da kuma kashi 70 na sabbin wadanda ke kamuwa," a cewar sakon bayan taron.

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Likitoci ta Najeriya, NMA, reshen jihar Zamfara ta sanar da cewa an tabbatar da cewa likitoci takwas sun kamu da coronavirus.

Mataimakin shugaban na NMA, Dr Mannir Bature ya shaidawa manema labarai a ranar Laraba cewa, "Cikin mutum 80 da suka kamu a jihar, kashi 10 cikin 100 likitoci ne da suka yi cudanya da majinyata.

"Muna farin cikin sanar da cewa cikin wadanda suka kamu, kashi 60 cikin 100 sun warke an sallame su yayinda sauran suna samun sauki," in ji shi.

Dr Bature ya kuma ce wasu likitoci 30 da suka yi cudanya da abokan aikinsu da suka kamu da cutar ta korona sun killace kansu domin kare yaduwar cutar a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel