Rundunar sojin Najeriya ta yi rashin dakaru 3 sakamakon harin 'yan ta'adda (Hotuna)

Rundunar sojin Najeriya ta yi rashin dakaru 3 sakamakon harin 'yan ta'adda (Hotuna)

Dakarun sojin Najeriya uku ne suka rasa rayukansu yayin fatattakar 'yan ta'adda, wani jami'i ya sanar.

Shugaban fannin yada labarai na ma'aikatar tsaro, John Enenche, ya bayyana a wata takarda da ta fita a ranar Laraba cewa sojoji uku ne suka rasa rayukansu yayin fatattakar 'yan ta'adda.

Manjo Janar Enenche, ya ce dakarun na daga cikin rundunar Operation Kantana Jimlan wadanda ke sintiri a tsakanin Buni Yadi da Buni Gari na jihar Yobe.

Sun ci karo da abubuwa masu fashewa ne a yayin da suka fatattaki mayakan ta'addancin a ranar Lahadi, jaridar Premium Times.

Rundunar sojin Najeriya ta yi rashin wasu dakarunta sakamakon harin 'yan ta'adda (Hotuna)
Rundunar sojin Najeriya ta yi rashin wasu dakarunta sakamakon harin 'yan ta'adda (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

Ya ce al'amarin ya faru ne a wuri mai nisan kilomita da wani gari da ke karamar hukumar Gujba da ke jihar Yobe yayin da sojoji ukun suka samu raunika sakamakon fashewar bam.

Kamar yadda yace, an kwashesu a motar daukar marasa lafiya amma sai suka sake taka wani abu mai fashewa inda wuta ta kama motar.

"An halaka 'yan bindiga uku yayin da wasu suka tsere da raunika masu tarin yawa," Enenche yace.

A wata takarda da ta bayyana nasarorin da rundunar sojin ta samu a kan 'yan ta'addan, an gano cewa dakarun sojin sama sun tarwatsa ma'adanar makaman 'yan ta'addan a yankin Njimia da ke dajin Sambisa a jihar Borno.

Rundunar sojin Najeriya ta yi rashin wasu dakarunta sakamakon harin 'yan ta'adda (Hotuna)
Rundunar sojin Najeriya ta yi rashin wasu dakarunta sakamakon harin 'yan ta'adda (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bude masallatai: Majalisar malaman Kano ta yi zazzafan martani ga Ganduje

Rundunar sojin Najeriya ta yi rashin wasu dakarunta sakamakon harin 'yan ta'adda (Hotuna)
Rundunar sojin Najeriya ta yi rashin wasu dakarunta sakamakon harin 'yan ta'adda (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

Farmakin da sojin saman Najeriya karkashin rundunar Operation Lafiya Dole ta kai a Njimia da ke dajin Sambisa, ya tarwatsa kayan yakin 'yan ta'addan Boko Haram.

Hari ta jiragen saman yakin da dakarun suka kai a ranar Talata ya biyo bayan rahotannin sirrin da suka samu a kan makaman 'ya ta'addan, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda bayanan suka nuna, wurin adanar makaman na nan a kusa da inda mayakan ke amfani da shi a matsayin sansani.

Suna ajiye man fetur da sauran kayayyakin bukata, kamar yadda takardar da Manjo Janar John Enenche ya fitar ta bayyana.

Ya ce babu kuskure harin da suka kai ya samu inda suka saita tare da tashin yankin. A take kuwa ma'adanar makaman suka kurmushe tare da yin mummunar barna ga mazaunin 'yan ta'addan.

Rundunar sojin Najeriya ta yi rashin wasu dakarunta sakamakon harin 'yan ta'adda (Hotuna)
Rundunar sojin Najeriya ta yi rashin wasu dakarunta sakamakon harin 'yan ta'adda (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel