Borno: Zulum ya amince da yin sallar Idi, ya gindaya sharudda 4

Borno: Zulum ya amince da yin sallar Idi, ya gindaya sharudda 4

Kwamitin yaki da muguwar cutar korona ta jihar Borno karkashin shugabancin mataimakin gwamnan jihar, Umar Usman Kadafur, ya bayyana amincewarsa a kan yin sallar idi na wannan shekarar a jihar.

An kai ga wannan matsayar ne bayan Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bada umarnin tuntubar Shehun Borno tare da yin taron malamai da limamai na jihar don samun matsaya.

Daga nan ne aka samu matsaya tare da gindaya wasu sharudda sannan amincewar ta biyo baya.

Kamar yadda kwamishinan lafiya na jihar Borno, Salihu Aliyu Kwaya Bura ya fitar a wata takarda, ya ce "mai girma mataimakin gwamnan jihar Borno kuma shugaban kwamitin yaki da cutar korona na jihar Borno, Alhaji Umar Usman Kadafur,

"A madadin Gwamna Babagana Umara Zuluma na farin ciki tare da yi wa jama'ar jihar Borno barka da azumi.

"Kwamitin na mika godiya ga dukkan 'yan jihar sakamakon hadin kai da goyon baya da suka bada wajen yaki da annobar a jihar."

Borno: Zulum ya amince da yin sallar Idi, ya gindaya sharudda 4
Borno: Zulum ya amince da yin sallar Idi, ya gindaya sharudda 4. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mun gano dalilin mace-mace a arewacin Najeriya - Dr Gwarzo

Kadafur ya bayyana cewa, akwai yuwuwar wasu matakan da aka dauka sun matukar takura wasu daga cikin jama'a, amma a sani, babu niyyar cutarwa game da hakan kuma saboda kiwon lafiya ne hakan ta faru.

A cewarsa, bayan tattaunawa da suka yi da malamai da limamai, sun kai ga matakai kamar haka:

1. Cewa jama'a za su yi sallar Idi a filayen sallolin idin jihar daga karfe 8 zuwa 10 na safiyar ranar idin.

2. Don kiyayewa tare da dakile yaduwar muguwar cutar, kwamitin ya samar da sinadaran tsaftace hannu don amfanin jama'a.

3. Kwamitin na kara jaddada cewa dole ne jama'a su fito sallar idin da takunkumin fuska tare da kiyaye dokar nesa-nesa da juna.

4. Kwamitin ta na shawartar tsoffin da suka kai shekaru 60 a duniya da kuma masu wasu ciwuka kamar su, asma, ciwon sukari, da sauransu da kada su fito sallar Idin.

"Muna fatan Allah ya karba ibadunmu kuma muna muku barka da sallah", mataimakin gwamnan ya rufe da addu'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel