Majalisar zartarwa ta amince da ayyukan N1.33bn a jami'ar Filato da Hukumar Kwastam

Majalisar zartarwa ta amince da ayyukan N1.33bn a jami'ar Filato da Hukumar Kwastam

Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), ta amince da bukatun da ma’aikatar ilimi da ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa suka shigar, na gudanar da wasu muhimman ayyuka na sama da N1,348,057,600.

Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, shi ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a ranar Laraba, 20 ga watan Mayu.

Da yake bayani dalla dalla a kan amincewar da majalisar ta yi, Ministan ya ce ma'aikatar ilimi za ta kashe N610, 355, 221.82 wajen ginin sabon reshen nazarin kiwon lafiya a jami'ar jihar Filato, Bokkos.

Haka kuma ma'aikatar ilimin za ta batar da N114, 357, 600 wajen sayen kayayyakin da za a kawata sabon reshen na jami'ar da sauran kayayyakin bukata da za a wadata shi da su.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, za a kammala sabon reshen nazarin kiwon lafiya na jami'ar ta Filato cikin makonni 12 inji Ministan.

Haka zalika majalisar zartarwas ta amince da bukatar da ma'aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasar ta shigar, na sayen kwamfutoci da na'urorin dab'i (printers) da za a wadata rassan hukumar fasakauri a kan N623, 700, 000.

Alhaji Mohammed ya ce ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, ita ta gabatar da bukatar haka a zauren majalisar da cewa a kashe N623, 700, 000 wajen sayen kwamfutoci da na'urorin dab'i guda 1, 200.

KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Sama da mutane 500 aka kashe a jihohi 10 cikin watanni 3

Ministar kudin kasar ta ce za a wadata dukkanin shiyoyin hukumar kwastam da ke fadin Najeriya da na'urorin domin inganta ayyukansu na gudanar da harkokin kudi da albarkatu.

Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar gwamnatinsa ta Aso Villa da ke babban birnin Tarayya na Abuja.

Wannan shi zaman majalisar na biyu da shugaban kasar ya jagoranta ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa da juna, wadda ta zama doka ta farko da aka fara bi tun a zaman majalisar na makon da ya gabata.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, 'yan majalisar kalilan ne suka hallara a zauren da ake gudanar da taron, yayin da da dama suka halarta ta hanyar bidiyo da aka hada da yanar gizo.

Majalisar ta zabi sauya salon zaman majalisar ne ta hanyar ba da tazara domin kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar'anta da manufar dakile yaduwar cutar korona wadda ta zamto ruwan daren da ya game duniya.

Ministocin da a dole su na da ta cewa kuma su na dauke da bayanan da za su gabatar su ne kadai suka halarci zaman majalisar a fadar shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel