Kano: Ganduje ya yi wa majami'un jihar feshi, ya saka wa CAN sharadi

Kano: Ganduje ya yi wa majami'un jihar feshi, ya saka wa CAN sharadi

Gwamnatin jihar Kano ta yi wa majami'u 31 na jihar feshin hana yaduwar cutar coronavirus, Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana.

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin taron da yayi da kungiyar mabiya addinin Kirista ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kano a gidan gwamnatin jihar.

Kamar yadda yace, hadin kan mabiya addinin Kiristan da masu ruwa da tsaki ya zama dole wajen shawo kan annobar a jihar.

Gwamnan ya yi kira ga shugabannin da sauran mazauna jihar da su kiyaye dokokin masana kiwon lafiya, jaridar Daily Nigerian ta wallafa.

Gwamna Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin za ta samar da dakin gwajin muguwar cutar a Sabon-Gari don bai wa mazauna yankin damar yin gwajin.

Gwamnan ya jinjinawa shugabancin CAN ta yadda suke karfafa guiwa wajen kiyaye dokar nesa-nesa da juna da sauran dokokin masana kiwon lafiya a coci.

Ganduje ya jaddada cewa wannan annobar ta shafi kowanne bangare na rayuwa.

Kano: Ganduje ya yi wa majami'un jihar feshi, ya saka wa CAN sharadi

Kano: Ganduje ya yi wa majami'un jihar feshi, ya saka wa CAN sharadi. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Boko Haram: Sojojin Najeriya sun kashe dandazon 'yan ta'adda a Yobe

"Ya shafe mu a addinance, al'adance, zamantakewa da tattalin arzikinmu.

"Duk da muna cikin wata mai alfarma, mun kasa zuwa masallatai don sallah.

"Abun takaici ne yadda bamu iya sallolin farillar mu a masallatai amma bamu da yadda zamu yi. Dole hakura zamu yi. Bamu iya gaisawa da hannu amma dole muka hakura," yace.

Shugaban CAN na jihar, Rabaren Samuel Adeyemo ya mika godiyarsa ga gwamnan a kan feshin da yayi wa majami'u 31 na jihar da sauran wuraren bauta.

Ya jinjinawa gwamnan da yadda ya sassauta dokar takaita zirga-zirga har da ranakun Lahadi don bai wa Kiristoci damar yin bauta.

Adeyemo ya ce majami'u na kiyaye dokar nesa-nesa da juna da sauran dokokin masana kiwon lafiya.

A wani labari na daban, dakarun sojin saman rundunar Operation Lafiya Dole sun halaka 'yan ta'addan Boko Haram da har yanzu ba a san yawansu ba.

Dakarun sun tarwatsa motocin yakinsu har biyu a wajen garin Dapchi da ke jihar Yobe.

A wata takarda da shugaban fannin yada labarai na rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar John Enenche ya fitar, ya ce sun yi aikin ta jiragen sama na yaki ne bayan samun rahoto cewa mayakan Boko Haram sun kai wa garin hari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel