Babu ranar sassauta dokar kulle a jihar Kaduna - El-Rufa'i

Babu ranar sassauta dokar kulle a jihar Kaduna - El-Rufa'i

Kawo yanzu kusan watanni biyu kenan da shimfida dokar hana fita a jihar Kaduna, gwamna Nasir El-Rufa'i ya yi karin haske kan yiwuwar sassauta dokar.

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i, ya yi watsi da yiwuwar sassauta dokar kullen da ya shimfida a jihar a yunkurin dakile yaduwar cutar korona.

Malam El-Rufa'i a ranar Talata, 19 ga watan Mayu, ya ce ba zai yi gaggawar cire dokar kullen da ya shimfida ba a jihar a sanadiyar yadda ba a samu wani rangwami ba na yaduwar cutar korona.

Tun a ranar 26 ga watan Maris ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirga, inda kuma a ranar 26 ga watan Afrilu, ta sake tsawaita dokar har na tsawon kwanaki 30.

Gwamnan jihar Kaduna; Mallam Nasir El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna; Mallam Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

Tsohon Ministan na Abuja ya hau kujerar naki tare kawar da kai a kan rokonsa da ake ci gaba da yi na neman a sassauta dokar kullen domin samun damar gudanar da Sallar Idi, wadda ake sa ran kasancewarta a ranar Asabar ko Lahadi.

A sanadiyar haka ma ya ce shi da kansa zai fita ya tsare iyakar Kano da Kaduna domin tabbatar da an kiyaye dokar hana zirga-zirga a ranar Sallah.

Gwamnan ya ce zai yi hakan ne domin ya tabbatar babu wani mutum da zai shigo Kaduna daga Kano.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Kogi ta hana mu gwajin masara lafiya da suka nuna alamun cutar korona - Likitoci

Ya ce gwamnatinsa ta na ci gaba da shirin sassauta dokar kullen, sai dai fa babu rana domin kuwa ya danganta da yadda lamari na annobar korona zai kasance.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Gwamnan yana cewa: "Ku duba sauran sassa na duniya, ko shugaban kasar Amurka, Donald Trump da ya ce zai cire dokar hana zirga-zirga, har yanzu bai kai ga cirewa ba."

"Wasu kasashen da a yanzu suka fara sassauta dokar kullen kuma sun fara fahimtar kuskure da sakamakon hukuncin da suka yanke" inji gwamnan.

Gwamnan yayin wata hira cikin harshen Hausa da wasu zababbun gidajen Rediyo a Kaduna suka yada, ya ce ba zai sassauta dokar kulle a jiharsa ba har sai an kara yawan cibiyoyin gwajin gano masu cutar korona kuma an daina zirga-zirga tsakanin jihohi gaba daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel