Gwamnatin Kogi ta hana mu gwajin marasa lafiya da suka nuna alamun cutar korona - Likitoci

Gwamnatin Kogi ta hana mu gwajin marasa lafiya da suka nuna alamun cutar korona - Likitoci

Likitoci a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke birnin Lokoja a jihar Kogi, sun zargi gwamnatin Yahaya Bello da kawo musu cikas na hana gwajin marasa lafiya da suka nuna alamun cutar korona.

Likitocin sun ce gwamnatin jihar tana mayar da hannun agogo baya a yayin da take ci gaba da kawo tangarda ta kin bari a gwada marasa lafiyan duk da sun nuna alamun cutar korona.

Kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa, ana zargin gwamnatin jihar Kogi ta hana ruwa gudu da manufa ta rashin ta a dole ba za a samu masu cutar korona ba a jihar.

Cikin wani rahoto da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a ranar Lahadi, 17 ga watan Mayu, ta ce mutum daya kawai a ka yiwa gwajin cutar korona a duk fadin jihar kuma sakamakonsa ya nuna ba ya dauke da kwayoyin cutar.

Wannan rahoto ya zo ne sabanin ikirarin da gwamnatin jihar ta yi na cewa an yi wa mutum 111 gwaji kuma dukkaninsu an tabbatar ba sa dauke da kwayoyin cutar.

Da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Talata, shugaban kungiyar likitoci na jihar Kogi, Agwu Nnanna, ya ce rashin aiwatar da gwajin gano masu cutar korona a jihar yana jefa ma'aikatan lafiya cikin barazana mai mugunyar hatsari.

Gwamnan jihar Kogi; Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi; Yahaya Bello
Source: Twitter

Ya ce akwai mutane da dama masu fama da matsananciyar rashin lafiya kuma alamomin cutar korona sun bayyana a tattare da su, amma jami'an da gwamnatin jihar ta wakilta sun hana a gwada su.

Nnanna ya yi kira ga Ma'aikatar Lafiya ta Tarayya da kuma kwamitin kula da cutar korona a Najeriya, da su kawo dauki jihar Kogi domin tabbatar da ana gwajin gano masu cutar ko ma'aikatan lafiyar jihar za su ji sanyi a ransu.

KARANTA KUMA: Na san Buhari ba zai iya magance matsalolin Najeriya ba - Yakasai

Makonni biyu da suka gabata ne Gwamnatin jihar Kogi ta ce ta gano tuggun da ake kullawa na neman ta dole sai an shigo da kwayoyin cutar korona cikin jihar ta kowace irin haramtacciyar hanya.

Gwamnatin jihar ta ce wannan yana daya daga cikin makarkashiyar da ake kulla wa na neman sai an tursasawa kowace jiha a fadin Najeriya samun bullar cutar korona.

Ta yi zargin cewa "a baya-bayan nan akwai miyagun da ke ci gaba da matsin lamba ta lallai sai an lalubo masu cutar tare da kaddamar da bullar ta a jihar."

A rahoton da jaridar Premium Times ta ruwaito, gwamnatin Kogi ta yi zargin yadda wasu masu wannan mummunar bukata ke huro wutar ayyana samun bullar cutar a jihar.

Sai dai fa gwamnati jihar ba ta fayyace ainihin masu neman kulla tuggun da zai shuka wannan mummunar badakala ba.

Cikin sanarwar da kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo ya fitar, ya yi zargin cewa, akwai yunkurin sai lallai an shigo da wannan annoba jihar Kogi.

Jihar da ke yankin Arewa ta Tsakiya, tana kewaye ne da jihohin da tuni suka samu bullar annobar ta korona.

A yanzu haka jihar tana ci gaba da fafatawa da gwamnatin tarayya dangane da yadda har kawo yanzu ta ke ikirarin bata samu bullar cutar ba.

Gwamnatin jihar cikin sanarwar da ta fitar ta bayyana cewa, babu yadda za a yi ta fidda bayanan karya ko kuma ta yi kagen samun bullar cutar domin biyan bukatar wasu jami'an lafiya da bata ambaci sunansu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel