Bude masallatai: Majalisar malaman Kano ta yi zazzafan martani ga Ganduje

Bude masallatai: Majalisar malaman Kano ta yi zazzafan martani ga Ganduje

Majalisar malaman jihar Kano ta ce kamata yayi gwamnati ta yi tunani kafin yanke hukuncin dawo da gabatar da sallar Juma'a da idi a jihar saboda yuwuwar yaduwar cutar korona.

Mallam Ibrahim Khalil, shugaban kungiyar majalisar malaman Kano, ya sanar da BBC cewa gwamnatin jihar ba ta tuntubesu ba a yayin yanke wannan hukuncin nata. Amma ya kamata a ce ta yi la'akari da bukatar jama'a.

Kamar yadda malamin ya bayyana, ya ce ya zama dole a kan gwamnati ta duba damuwar jama'arta da kuma abinda ya dace, tunda bata tuntubi majalisar malamai ba.

A cewarsa, "Amma irin wannan yanayi na annoba da ake ciki, duk wanda yake jin tsoron cewar zai kamu da cutar idan yaje masallacin ko kuma zai zama hadari, to zai iya zamansa a gida."

Amma wanda kuma yake ganin shi zai iya zuwa masallacin ba tare da wata matsala ba, to shi wannan zai iya zuwa masallaci ya yi sallah in ji malamin.

Ya kara da cewa, "Batun a ce duk wanda bai je masallaci ba ya aikata zunubi, to gaskiya ba haka bane in dai akwai dalili mai karfi."

Bude masallatai: Majalisar malamai ta yi zazzafan martani ga Ganduje

Bude masallatai: Majalisar malamai ta yi zazzafan martani ga Ganduje. Hoto daga The Cable
Source: Facebook

KU KARANTA: Kano: Ganduje ya bude dakin gwaji na musamman don Kiristocin jihar

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi wa malaman da suka zargesa da hana sallar Juma'a a jihar 'Allah ya isa'.

Gwamnan ya ce ya bar malaman da Allah ne a jawabin da ya yi ga 'yan jiharsa a yammacin Talata.

A cewarsa, "Ko a makka ba za a yi sallar idi ba amma mu a nan malamai sun hau mumbari suna cewa mun hana sallah. Saboda haka Allah ya isa. Na yafe wa duk wanda ya zage ni amma ba zan yafe wa wanda yayi min kazafi ba."

Gwamnan ya tabbatar da cewa ba zai bar kowanne mutum shiga jihar Kaduna a ranar Sallah daga Kano ba. Kasancewar gwamnatin jihar Kano ta amince da gudanar da sallar Idi da Juma'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel