Covid-19: Sabbin mutum 226 sun kamu a Najeriya, jimilla 6401

Covid-19: Sabbin mutum 226 sun kamu a Najeriya, jimilla 6401

Sabbin alkalluma da hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a Najeriya, NCDC ta fitar a daren Talata sun nuna cewa masu dauke da korona yanzu haka a kasar sun kai 6,401.

Hakan ya biyo bayan samun karin sabbin mutum 226 da suka sake kamuwa da cutar a cikin sa'o'i 24 da suka shude.

Hukumar ta wallafa alakallumar ne a shafinsa na dandalin sada zumunta na Twitter kamar yadda ta saba a kullum.

Yanzu dai jimilar wadanda da cutar ta kashe a fadin kasar ya kai 192, yayin da mutum 1,734 suka warke kuma aka sallamesu.

A Legas, jihar da ta fi yawan masu fama da Covid-19, sabbin alkaluma sun nuna an sake samun mutane 131 da suka harbu.

Jihar Ogun ita ce ta biyu a jadawalin daren Talata da mutane 25 sabbin kamu.

Sai Plateau mai 15, Edo 11, Kaduna 7, Oyo 6, Abuja da Adamawa kowannensu 5.

Jigawa, Ebonyi da Borno kowannensu mutum 4 sai Nasarawa an samu sabbin mutum 3.

Gombe da Bauchi an samu mutum 2,2 sai Enugu da Bayelsa kowannensu 1,1.

DUBA WANNAN: Daya daga cikin mambobin FCC 37 da Buhari ya nada ya mutu kafin rantsar da su

A wani labarin, kun ji cewa wata mata mai shekaru 22 cikin wadanda suke jinyar COVID-19 a Legas ta haifi tagwaye a Asibitin Koyarwa ta Jamiar Legas (LUTH).

Mai jinyar ta haifi mace da na miji a ranar Talata 19 ga watan Mayu, hakan ya kawo jimillar jariran da aka haifa a asibitin zuwa hudu.

Asibitin ya tabbatar da haihuwar tagwayen cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Twitter.

Sakon ya ce, "Tawagar likitoci a LUTH da masu kula da numfashi da jamian jinyan a yau Talata, 19 ga watan Mayun 2020 sun taimakawa wata mata mai shekaru 22 da ke dauke da COVID-19 ta haifi tagwaye mace da na miji.

"Nauyin jariran a lokacin da aka haife su kilogram 3.2 na miji sai macen kilogram 3.25, matar ta haihu ne ta hanyar tiyata. "Mahaifiyar da jariran duk suna cikin koshin lafiya!”.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel