Boko Haram: Sojojin Najeriya sun kashe dandazon 'yan ta'adda a Yobe

Boko Haram: Sojojin Najeriya sun kashe dandazon 'yan ta'adda a Yobe

Dakarun sojin saman rundunar Operation Lafiya Dole sun halaka 'yan ta'addan Boko Haram da har yanzu ba a san yawansu ba.

Dakarun sun tarwatsa motocin yakinsu har biyu a wajen garin Dapchi da ke jihar Yobe.

A wata takarda da shugaban fannin yada labarai na rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar John Enenche ya fitar, ya ce sun yi aikin ta jiragen sama na yaki ne bayan samun rahoto cewa mayakan Boko Haram sun kai wa garin hari.

Ya ce an tura jirgin yakin ne wurin motocin 'yan ta'addan sannan sun samu sa'ar tashin motoci biyu tare da halaka wasu 'yan ta'addan.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan ta'addan sun kai hari Dapchi, babban birnin karamar hukumar Bursari a daren Litinin.

Maharan sun banka wa fadar hakimin garin wuta, sun balle shaguna tare da yin awon gaba da kayan abinci da sauran kayayyakin amfani na 'yan kauyen.

An gano cewa sun tsinkayi kauyen ne a yayin da Musulmai ke buda bakin azumin da suka kai na watan Ramadan.

Boko Haram: Sojojin Najeriya sun kashe dandazon 'yan ta'adda a Yobe

Boko Haram: Sojojin Najeriya sun kashe dandazon 'yan ta'adda a Yobe. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gambari ya ajiye mukaminsa a SCDDD

A wani labari na daban, gwamnatin Jihar Kwara ta yi rashin wakilin ta da Shugaba Buhari ya zaba domin nada shi mamba a Hukumar Daidaito a Ayyukan Gwamnatin Tarayya (FCC), James Kolo.

Marigayi Kolo ya rasu ne a ranar Talata a Asibitin Koyarwa ta Jamiar Ilorin (UITH) bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Dan asalin garin Patigi ne a karamar hukumar Patigi na jihar.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar ta mika sakon taaziyarsa da mutanen garin Patigi da yayan All Progressives Congress (APC) game da rasuwar dan siyasan.

AbdulRazaq, a cikin sanarwar da hadiminsa Rafiu Ajakaye ya fitar ya bayyana Patigi a matsayin mutum mai yi wa jamiyya biyayya kuma mai kaunar aiki tare da mutane wadda rasuwarsa babban rashi ne ga iyalansa, mutanen karamar hukumar Patigi da jihar baki daya.

Gwamnan ya ce, "Munyi bakin cikin rasuwar Mr Kolo da ya mutu bayan rashin lafiya. Mutum ne mai kaunar jamiyya kuma mai sada zumunci da ya yi aiki tukuru tare da wasu masu kishin jam'iyya domin ganin APC ta yi nasara a jihar. "

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel