Na san Buhari ba zai iya magance matsalolin Najeriya ba - Yakasai

Na san Buhari ba zai iya magance matsalolin Najeriya ba - Yakasai

Daya daga cikin Dattawan Arewa, Alhaji Tanko Yakasai, ya bayyana dalilan da suka sanya bai taba fatan ganin shugaba Muhammadu Buhari ba a kujerar mulkin Najeriya.

Tsohon sakataren jam'iyar NEPU na kasa, ya fayyace babban dalilin da ya sanya bai taba kuskuren goyon bayan kasancewar shugaba Buhari ba a kujerar gwamnatin kasar nan.

Alhaji Yakasai ya ce cikakkiyar fahimtar da ya yi wa Buhari ta rashin cancantarsa na gyara matsalolin kasar nan ya sanya bai taba fatan an waye gari ya zama jagora ba a Najeriya.

Ya ce, fahimtar da ya yi wa Buhari ta cewa da shi da babu a kujerar gwamnatin kasar nan duk abu daya ne, ta sanya bai taba burin ya ga rike akalar jagorancin Najeriya ba.

Ya kara da cewa babu wani abu sabo ko kuma na ba zata da bai yi tsammani ba a tsawon shekaru biyar da shugaba Buhari ya shafe a kan gado na mulkin kasar nan.

Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Kano ya ce, sam babu wani mamaki da ya yi dangane da yadda Gwamnatin Buhari ta jagoranci kasar nan a tsawon shekaru biyar da shude, lamarin da ya ce komai ya yi daidai da tsammaninsa.

Alhaji Tanko Yakasai

Alhaji Tanko Yakasai
Source: UGC

Yakasai wanda kuma ya kasance tsohon kwamishinan kudi na jihar Kano, ya yi furucin hakan ne yayin da ya bayyana a wani zaman ganawa ta bidiyo da kungiyar tabbatar da ingancin jagoranci a duniya, Governance index, ta dauki nauyi.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa, Governance index ta dauki nauyin wannan taro a ranar Juma'a wanda kusan mutum 100 suka halarta daga sassa daban-daban a fadin duniya.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Kano ta gindaya sharudan gudanar da Sallar Juma'a da Idi

Ya ce har yanzu Buhari ya gaza kunyata shi wajen tabbatar masa da cewa ya cancanci riko da tafiyar da al'amuran kasar nan.

“Ban taba goyon bayan Buhari ba. A koda yaushe adawa nake da shi saboda na san bai cancanci ya rike shugabancin Najeriya ba, kuma a kullum yana kara tabbatar min da gaskiyar hakan."

"Lokacin da aka zabi Buhari a matsayin shugaban Najeriya, na yi tsammanin ko da matsalar wutar lantarki gwamnatinsa za ta iya kawo karshen ta a kasar nan, amma har yanzu babu amo ballantana labarin wutar lantarki ta daidaita."

"Yanzu yana cikin shekararsa ta biyar kenan, cikakkun shekaru biyu ne kacal suka rage masa a wa'adinsa domin kuwa babban zaben kasa ne zai lakume ragowar shekarar ta karshe."

"Ban san irin shiri ko tsare-tsaren da ya yi wa kasar nan tanadi ba, har yaushe za a samu wadatacciyar wutar lantarki a jihar Kano da za ta dawo da martabar masana'antu a jihar, ta yadda kowane mutum a Kano zai samu abun yi."

"Hakan kuma take a jihar Enugu, Legas da sauran jihohin da masana'antunsu suka durkushe."

"Rashin wutar lantarki na daya daga cikin manyan matsalolin da kasar nan take fuskanta tun daga lokacin da aka zabi Buhari kawo yanzu, kuma har yanzu su ne dai kalubalen da ake fuskanta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel