Daya daga cikin mambobin FCC 37 da Buhari ya nada ya mutu kafin rantsar da su

Daya daga cikin mambobin FCC 37 da Buhari ya nada ya mutu kafin rantsar da su

Gwamnatin Jihar Kwara ta yi rashin wakilin ta da Shugaba Buhari ya zaba domin nada shi mamba a Hukumar Daidaito a Ayyukan Gwamnatin Tarayya (FCC), James Kolo.

Marigayi Kolo ya rasu ne a ranar Talata a Asibitin Koyarwa ta Jamiar Ilorin (UITH) bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Dan asalin garin Patigi ne a karamar hukumar Patigi na jihar.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar ta mika sakon taaziyarsa da mutanen garin Patigi da yayan All Progressives Congress (APC) game da rasuwar dan siyasan.

Wani da za a nada Kwamishina ya rasu a Kwara

Wani da za a nada Kwamishina ya rasu a Kwara. Hoto daga The Nation
Source: UGC

KU KARANTA: COVID-19: An kama Janar din Soja da malamin addinin musulunci a Kaduna

AbdulRazaq, a cikin sanarwar da hadiminsa Rafiu Ajakaye ya fitar ya bayyana Patigi a matsayin mutum mai yi wa jamiyya biyayya kuma mai kaunar aiki tare da mutane wadda rasuwarsa babban rashi ne ga iyalansa, mutanen karamar hukumar Patigi da jihar baki daya.

Gwamnan ya ce, "Munyi bakin cikin rasuwar Mr Kolo da ya mutu bayan rashin lafiya. Mutum ne mai kaunar jamiyya kuma mai sada zumunci da ya yi aiki tukuru tare da wasu masu kishin jam'iyya domin ganin APC ta yi nasara a jihar.

"Mun gode wa Allah cewa shi mutumin kirki ne da ba shi da abokin gaba. Mutane da yawa sun san shi a matsayin mutum mai yawan kyauta.

"Muna mika taaziya ga iyalansa tare da adduar Allah ya basu hakurin jure rashinsa ya kuma gafarta masa."

A wani labarin, kun ji cewa wata mata mai shekaru 22 cikin wadanda suke jinyar COVID-19 a Legas ta haifi tagwaye a Asibitin Koyarwa ta Jamiar Legas (LUTH).

Mai jinyar ta haifi mace da na miji a ranar Talata 19 ga watan Mayu, hakan ya kawo jimillar jariran da aka haifa a asibitin zuwa hudu. Asibitin ya tabbatar da haihuwar tagwayen cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Twitter.

Sakon ya ce, "Tawagar likitoci a LUTH da masu kula da numfashi da jamian jinyan a yau Talata, 19 ga watan Mayun 2020 sun taimakawa wata mata mai shekaru 22 da ke dauke da COVID-19 ta haifi tagwaye mace da na miji.

"Nauyin jariran a lokacin da aka haife su kilogram 3.2 na miji sai macen kilogram 3.25, matar ta haihu ne ta hanyar tiyata. "Mahaifiyar da jariran duk suna cikin koshin lafiya!”.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel