Gwamnatin Kano ta gindaya sharudan gudanar da Sallar Juma'a da Idi

Gwamnatin Kano ta gindaya sharudan gudanar da Sallar Juma'a da Idi

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya amince a ci gaba da gudanar da sallolin Juma’a da kuma sallar Idi, duk da gwamnatin tarayya ta tsawaita dokar zaman gida a jihar.

Ana iya tuna cewa, a ranar Litinin da ta gabata ne gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ta ba da umarnin tsawaita dokar kulle a Kano har na tsawon makonni biyu.

Mashawarcin gwamnan a kan sabbin hanyoyin sadarwa na zamani, Salihu Tanko Yakasai, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, ya ce a yanzu gwamnatin Kano ta sake nazari a kan dokar takaita zirga-zirga.

A baya dai an sassauta wa al'ummar Kano dokar kulle a ranakun Litinin da Alhamis na kowane mako.

Sanarwar da hadimin gwamnan ya wallafa a kan shafin sa na Facebook ta bayyana cewa, gwamna Ganduje ya sahalewa al'ummar Kano damar ci gaba da yin Sallolin Juma'a da Sallar Idi.

Gwamnan Kano; Abdullahi Ganduje
Hakkin mallaka: Salihu Tanko Yakasai

Gwamnan Kano; Abdullahi Ganduje Hakkin mallaka: Salihu Tanko Yakasai
Source: Facebook

Ana sa ran Sallar Idi ta karamar Sallar bana za ta kasance a ranar Asabar ko Lahadi, duk dai ranar da ta kasance 1 ga watan Shawwal a kalandar Musulunci.

Tanko Yakasai ya ce gwamnatin ta yanke shawarar hakan ne bayan wata doguwar tattaunawa da tayi da manyan Malaman Musulunci na jihar guda 30 a fadar gwamnatin.

KARANTA KUMA: Coronavirus: An fi samun yawan mace-mace a Legas, Kano da Borno - Mamora

Daga karshe gwamnan ya amince da shawarwarin da aka yanke yayin taron, inda ya amince a kan sassauta dokar kulle a ranakun Lahadi, Laraba da kuma Juma'a.

Sai dai Gwamnatin Kano cikin sanarwar da ta fito daga bakin Kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba, ta gindaya wasu sharudda da za a kiyaye a Masallatai.

Domin rage cunkoson jama'a, kwamishinan ya ce za a gudanar da sallar Idi a dukkanin masallatan da aka saba gudanar da sallolin idi a fadin jihar.

Sauran sharudan da gwamnatin ta gindaya sun hada da:

1. A takaice ba tare da an tsawaita yin doguwar huduba ba a Masallatai.

2. Duk wanda zai shiga Masallacin Juma’a sai ya sanya takunkumin rufe fuska.

3. Duk wanda zai shiga masallaci sai ya wanke hannayensa da ruwa da sabulu ko kuma sunadarin tsarkake hannu wato sanitizer.

4. A tabbatar an ba da tazara wurin hada sahu a cikin Masallatai.

5. Babu shagulgulan sallah irin su Hawan Sallah kamar yadda Sarakuna suka saba a lokuta na baya.

Daga karshe kuma Gwamnatin Kano ta kafa wani kwamiti da zai yi rabon kayan tsafta ga Masallatan gami da tabbatar da an kiyaye dukkanin sharudan da Gwamnatin ta gindaya.

Haka kuma Gwamnatin Saudiyya ta umarci al'ummar kasar da su gudanar da Sallar idin bana a gidajensu bayan samun dalilian wata sabuwar fatawa ta majalisar malaman kasar.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, shugaban majalisar Malaman kasar da ya ba da fatawar, Abdul Aziz Asheikh, ya ce ya halasta a gudanar da Sallar Idi a gida duba da annobar da ake fama da ita.

Haka zalika Shehin Malamin ya bayyana cewa, ita ma zakkar fidda kai ba sai an bi gida-gida ba duba da dokar zaman gida da aka sanya, lamarin da da ya ce za a iya bayarwa ta hannun kungiyoyin bayar da agaji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel