Gambari ya ajiye mukaminsa a SCDDD

Gambari ya ajiye mukaminsa a SCDDD

Shugaban ma'aiktan fadan shugaban kasan Najeriya, Farfesa Ibrahim Gambari ya yi murabus daga kejerarsa ta Shugaban Cibiyar Diflomasiyya, Demokradiyya da Cigaba ta Savannah (SCDDD).

A cewar babban sakataren cibiyar, Ambasada Abdullahi Omaki, Gambari ya aike da sakon murabus din ne nan take domin yana ganin hakan ya dace ya yi domin ya samu damar mayar da hankali kan aikinsa baki daya.

An kuma nada Mallam Abidu Yazid a matsayin sabon shugaban na Cibiyar ta Diflomasiyya da Cigaban Demokradiyya ta Savannah domin maye gurbin Gambari.

Gambari ya ajiye mukaminsa a SCDDD
Gambari ya ajiye mukaminsa a SCDDD. Hoto daga This Day
Asali: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Za a tura 'Yan Hisbah masallatai da filayen Idi a Kano

"Na isar da wannan sakon ga mambobin kwamitin gudanarwa kuma bayan tattaunawa sun amince da nada Mallam Abidu Yazid a matsayin sabon shugaban na Savannah Centre for Diplomacy, Democracy and Development (SCDDD).

"Ina son in sake taya Farfesa Gambari murna saboda hangen nesan sa na kafa wannan cibiya ta kwararru da ta bayar da muhimmiyar gudunmawa wurin tabbatar da demokradiya da kawo cigaba tun 2014.

"Tun kafa ta, Cibiyar ta bayar da gudanar da ayyuka da suka hada da shirya taron yin sulhu da nufin hada kan yan kasa, inganta shugabanci, tsaro a kasa da tattalin arziki da taimakawa gajiyayyu a kasar."

Yazid, kwararren masanin tattalin arziki ne kuma ya rike mukamai da dama a gwamnati har ya zama sakataren gwamnatin jiha da shugababan maaikatan jiha a tsohuwar jihar Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel