COVID-19: Muna tufka ne, jama'ar kasar nan suna warwarewa - Buhari

COVID-19: Muna tufka ne, jama'ar kasar nan suna warwarewa - Buhari

Gwamnatin tarayya ta nuna rashin jin dadinta da yadda ake samun sabani tsakanin wasu jihohi da kuma matakan da take dauka a kan yaki da korona a kasar nan.

Wannan korafin na zuwa ne bayan tsawaita dokar takaita zirga-zirga da gwamnatin tarayya ta yi wa jihar Kano na makonni biyu.

A ranar Litinin ne shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da wasu gwamnonin jihohi ta yanar gizo a kan yaki da cutar korona tare da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da tsaron kasar nan.

Shugaba Buhari ya nemi hadin kan jihohin inda yace gwamnatin tarayya na tufka amma wasu jihohin na warwarewa.

A tattaunawar da Malam Garba Shehu, mai taimakawa shugaban kan harkokin yada labarai da BBC, ya ce abin takaici ne a ce gwamnati na daukan matakan yaki da annobar amma tana rasa samun hadin kai.

COVID-19: Muna tufka ne, jama'ar kasar nan suna warwarewa - Buhari

COVID-19: Muna tufka ne, jama'ar kasar nan suna warwarewa - Buhari. Hoto daga Daily Trust
Source: Facebook

KU KARANTA: Kano: 'Yan sanda sun damke 'yan ta'adda 197 da miyagun makamai

Ya ce, "Ba wai zargi muke yi ba ko kushe, amma akwai bukatar a ce ana tafiya tare saboda idan ba a samu matsaya ba, da wuya a yi nasarar yakar annobar."

Garba ya kara da cewa, kwamitin da ke yaki da annobar na fadar shugaban kasa na koka wa a kan yadda matakan wasu jihohi ke warware nasarorinsu.

"Kamata yayi kafin a dauka kowanne irin mataki, to a tuntubi masana don neman shawarwari," cewarsa.

Kakakin ya ce bai wai ana ganin babu hadin kai daga gwamnonin bane, amma kowacce jiha na daukar matakin da ta ga ya dace ba tare da tuntubar kwararru ba.

Wannan batun na zuwa ne bayan sa'o'i kadan da jihar Kano ta yi wa sabuwar dokar shugaban kasa na yaki da cutar a jihar kwaskwarima.

A wani labari na daban, a kalla mutum 48 ne aka kashe a rikicin kabilanci da ya auku a karamar hukumar Lamurde ta jihar Adamawa.

Ana shirya gawawwakin da aka kashe sakamakon rikicin don yi musu jana'iza baki daya duk da kuwa ana tsammanin kara samun wasu gawawwakin, wata majiya ta sanar da SaharaReporters a ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi amfani da miyagun makamai a yayin rikicin a Tigno da ke karamar hukumar Lamurde.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel