Boko Haram: 'Yan ta'adda sun bankawa gidan hakimi wuta, ya kone kurmus

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun bankawa gidan hakimi wuta, ya kone kurmus

Wasu mayakan Boko Haram sun kai hari garin Dapchi tare da bude wuta wacce ta sa mazauna garin suka tsere zuwa daji.

Ba a san adadin mutanen da harin ya shafa ba a garin da ya sha fama da miyagun hare-haren Boko Haram tun a baya.

Wani mutum mazaunin Dapchi ya sanarwa BBC cewa, 'yan ta'addan sun isa garin ne da yammacin ranar Litinin, 18 ga watan Mayun 2020, inda suka bude wuta suna ta harbe-harbe.

Kamar yadda mutumin ya bayyana, "Ina cikin gida na ji harbi, lamarin da ya tsoratar da ni na gudu zuwa bayan gari. Na hadu da jama'a da dama wadanda suka tsero daga cikin garin."

Ya ce "A nan ne ake fada min cewa maharan sun kone gidan hakimi. Bayan na je wurin, na ga gidansa a kone kurmus."

Kamar yadda mutumin ya bayyana, kafin maharan su kone gidan, sun kwashe kayan sa wa da abinci. Daga bisani suka banka fetur tare da kone gidan.

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun bankawa gidan hakimi wuta, ya kone kurmus

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun bankawa gidan hakimi wuta, ya kone kurmus. Hoto daga HumAngle
Source: Twitter

KU KARANTA: Kano: 'Yan sanda sun damke 'yan ta'adda 197 da miyagun makamai

Ya ce, "Ko da maharan suka isa gidan hakimin, babu kowa a ciki don sun gudu bayan gari sakamakon harbi bindigar da suka ji."

Kamar yadda ya kara da cewa, bai ga gawa ko daya ba don kusan duk mutanen garin tserewa suka yi.

Amma daga karshe sojoji sun shiga garin bayan maharan sun shafe kusan sa'a guda.

A wani labari na daban, a kalla mutum 197 ne wadanda ake zargi da laifuka daban-daban da ya hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, satar motoci da kwacen adaidaita ne suka shiga hannun 'yan sandan jihar Kano.

An kama wadanda ake zargin tsakanin ranar 11 ga watan Mayu zuwa 15 ga watan Mayu a yankuna daban-daban na jihar.

Rundunar Operation Puff-Adder ne suka yi wannan kamen. DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, jami'in hulda da jama'a na rundunar ya bayyana hakan ga manema labarai a yammacin Juma'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel