Kano: Allah ya yi wa Farfesa Aliyu Danshehu Maiwada rasuwa

Kano: Allah ya yi wa Farfesa Aliyu Danshehu Maiwada rasuwa

Allah ya yi wa Farfesa Aliyu Danshehu Maiwada (ADM) rasuwa a ranar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya, wata majiya daga iyalan sa ta sanar.

Farfesa Maiwada tsohon malami ne a jami'ar Bayero dake Kano, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A ta'aziyyar da tsohon abokin aikinsa, Julius Afolabi Falola ya yi, ya kwatanta mamacin da mutum mai shiru-shiru, mai son zaman lafiya, mai wadatar zuci da kuma kula da iyalansa.

"Na san cewa duk da ka rasu, dalibai da masu bincike da za su karanta ayyukanka, za su matukar karuwa. Za su sanka a rubuce duk da ba za su taba ganinka ba," Farfesa Falola yace.

"ADM ya tafi, mun yi babban rashi. Addu'a kadai za mu iya yi, Allah ya bai wa iyalansa hakuri. Sai mun hadu abokin aiki," ya kara da cewa.

Ya rasu ya bar mata daya da 'ya'ya shida kuma tuni aka yi jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Kano: Allah ya yi wa Farfesa Aliyu Danshehu Maiwada rasuwa

Kano: Allah ya yi wa Farfesa Aliyu Danshehu Maiwada rasuwa. Hoto daga ees.buk.edu.ng
Source: Twitter

KU KARANTA: Rikicin kabilanci: Rayuka 48 sun salwanta a jihar Adamawa (Hotuna)

A wani labari na daban, a kalla mutum 48 ne aka kashe a rikicin kabilanci da ya auku a karamar hukumar Lamurde ta jihar Adamawa.

Ana shirya gawawwakin da aka kashe sakamakon rikicin don yi musu jana'iza baki daya duk da kuwa ana tsammanin kara samun wasu gawawwakin, wata majiya ta sanar da SaharaReporters a ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi amfani da miyagun makamai a yayin rikicin a Tigno da ke karamar hukumar Lamurde. An samu rashin rayuka masu tarin yawa da dukiyoyi.

SaharaReporters ta gano cewa, rikicin ya barke ne a daren Alhamis tsakanin asalin 'yan kabilar Chobok da kuma Hausawa, kamar yadda majiya daga yankin ta sanar.

An gano cewa, rikicin ya barke ne sakamakon fadan da ake yi na yanka Alade a mayankar garin. Daga nan ne aka fara fadan da ya janyo kashe-kashe.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma bai bada yawan jama'ar da suka rasa ransu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel