Da duminsa: Yan Boko Haram sun kai farmaki Daphi yanzu haka, suna kona gidaje

Da duminsa: Yan Boko Haram sun kai farmaki Daphi yanzu haka, suna kona gidaje

Yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram na kan kai hari garin Daphi, dake karamar hukumar Tarmuwa ta jihar Yobe. The Cable ta ruwaito.

An bayyana cewa yan ta'addan sun isa garin ne cikin motocin yaki misalin karfe 7 na yammacin Litinin.

Wani mazaunin garin, Bala Bukar, ya bayyanawa TheCable cewa yan ta'addan sun bankawa gidajen mutane wuta yayinda mutanen suka gudu daga muhallin domin ceton rayukansu.

Bukar ya ce tuni an tura jiragen yakin sojin sama cikin garin kuma Sojoji na kokarin kawar da su.

Yace: "Sojoji da yan ta'addan na musayar wuta yanzu. Yanzu haka da nike magana ana jefe-jefen bama-bamai."

"Yan ta'addan sun kwace gari. Yawancin mazaunin sun gudu."

Wani mazaunin daban wanda ya gudu garin Baymari, ya ce har gidan Maigarin an kona.

Ya ce watanni biyar kenan da aka janye jami'an tsaro daga garin.

Garin Dapchi ta fara kaurin suna ne a ranar 19 ga Febrairu, 2018 da yan ta'addan ISWAP sukayi garkuwa da yan matan makarantan sakandare 117.

Yayinda biyar suka mutu a tsare, an samu ceto sauran illa Leah Sharibu wacce suka rike saboda ta ki barin addininta.

Ku saurari cikakken rahoton....

Asali: Legit.ng

Online view pixel