Da duminsa: Shugaba Buhari ya shiga ganawar sirri da TY Danjuma (Hotuna)

Da duminsa: Shugaba Buhari ya shiga ganawar sirri da TY Danjuma (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka ya shiga ganawar sirri da tsohon ministan tsaron Najeriya, Janar Theophilus Danjuma a fadar Aso VIlla.

Janar Theophilus Danjuma ya rike kujeran ministan tsaro lokacin mulkin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo.

KU KARANTA: Da Buhari zai sake tsayawa takara babu mai zabensa - Jigo a APC, Dan Bilki Kwamnada

A baya-bayan nan, Janar Danjuma ya zama daya daga cikin yan adawan gwamnatin Buhari kan wasu lamura musamman tsaro.

Tsohon ministan ya zargi gwamnatin tarayya da Sojoji da hada kai da Fulani Makiyaya wajen kai hare-hare suna hallaka mutane.

Yayinda yake jawabi a wani taro a jami'ar Ibadan, jihar Oyo, Danjuma ya zargi shugabannin kabilar Yarbawa da tsoron sukar gwamnatin Buhari duk da cewa ya bayyana karara kasar na gab da rugujewa.

Ya ce hankulan yan Najeriya zasu tashi idan ya furta abubuwan da ya sani dake faruwa a kasar.

Danjuma yace: "A kasar Yarbawa, kowa ya yi shiru, ana tsoro. Kuma kamar mutane basu damu da abinda ke faruwa ba. Idan na fada muku abinda ke faruwa a Najeriya yau, ba zaku iya bacci ba."

"Idan kuna son bayanai filla-filla, zan baku a sirrance."

"Muna cikin babbar matsala a kasar nan....Saboda haka ya zama wajibi mu tashi tsaye."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel