'Yan fashi a jirgin sama sun kai hari kauyukan Neja, sun kashe fasto, makaho, da wasu mutum 3

'Yan fashi a jirgin sama sun kai hari kauyukan Neja, sun kashe fasto, makaho, da wasu mutum 3

Ta'addanci ya dauki wani sabon salo na daban a safiyar Lahadin da ta gabata, yayin da 'yan fashi suka yi amfani da jirgin sama mai saukar Angulu wajen kai hari kan a kalla kauyuka hudu a karamar hukumar Shiriro ta jihar Neja.

Wannan mummunan hari na bazata ya salwantar da rayukan mutum biyar kamar yadda jaridar The Sun ta bayar da shaida.

Cikin wadanda harin ta sama da kasa ya salwantar da rayukansu da safiyar Lahadin sun hadar da wani fasto, wanda aka kone cocinsa kurmus, wani mutum makaho da kuma wasu mutum uku.

'Yan fashin sun yi awon gaba da shanu sama da dubu daya daga cikin kauyukan guda hudu, wadanda mutane suka bayar da shaidar cewa maharan sun kai 50 haye a kan babura da ba a tantance yawansu ba.

Wata majiya da ke kusa da daya daga cikin kauyukan, ta shaida wa manema labarai cewa, wani jirgi mai saukar Angulu ya rika shawagi da kewaye a sararin samaniyan wadannan kauyuka a tsawon awanni ukun da maharan suka tashi hankalin al'umma.

'Yan fashi a jirgin sama sun kai hari kauyukan Neja, sun kashe fasto, makaho, da wasu mutum 3

'Yan fashi a jirgin sama sun kai hari kauyukan Neja, sun kashe fasto, makaho, da wasu mutum 3
Source: Twitter

Majiyar ta ce sun yi tsammanin jirgin ya kawo dauki ne ashe maharan ya ke kara wa karfin gwiwa ta cin karensu babu babbaka cikin nutsuwa da kwanciyar hankali har zuwa lokacin da suka kammala ta'addancin.

KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun kashe wani dan Kasuwa a Kano

Kauyukan da maharan suka kai wa hari yayin sabunta ta'addanci sun hadar da Nankusa, Nansa, Eburo da Lagodo, duk a karkashin gundumar Erena ta karamar hukumar Shiroro.

A wani yankin na kauyen Nansa, an ce 'yan fashin cikin fushi sun kone duk amfanin gonar da suka tarar cikin rumbunan sanadiyar yadda ba su tarar da kowa ba a kauyen.

Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen kauyen sun arce cikin dokar daji tun kafin 'yan ta'addan su cimma su.

A cewar majiyar, makahon ya yi gamo da ajali a hannun 'yan bindigar yayin da yake fitowa daga daji bayan bukata ta sa ya kewaya bayan gida, inda shi kuma aka harbe fasto din a kusa da cocinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel