Jami’an jinya su 70 sun kamu da cutar Coronavirus yayin da suke aiki a Asibitocin Najeriya
Akalla jami’an jinya da unguwar zoma guda 70 ne suka kamu da cutar Coronavirus daga cikin guda 600 da aka yi ma gwaji, inji shugaban kungiyarsu Abdurafiu Adeniji.
Daily Trust ta ruwaito Adeniji ya bayyana haka ne yayin bikin makon tunawa da jami’an jinya, inda yace mambobinsu 1,000 na cikin hadarin kamuwa da cutar, 200 na killace a yanzu haka.
KU KARANTA: Bayanai sun bayyana game da abin da ya sabbaba sallamar Sule Hunkuyi daga PDP
Adeniji ya kara da cewa ma’aikatan jinya da unguwar zoma 5 ne suka mutu a sanadiyyar cutar, sa’annan ya koka kan karancin adadin jami’an a asibitocin Najeriya.
A cewarsa, hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO, ta bayyana ana bukatar jami’an jinya 40 ga mutane 100,000, amma a Najeriya jami’an jinya 5 ne ga mutane 100,000.
“Hadarin COVID-19 ta shafi jami’an jinya da unguwar zoma da dama saboda fargaba, rashin kayan kariya, damuwa, rashin magunguna, rashin kayan ceton rai, babu inshoran rai da matsalar zirga zirga.
“Akwai cin zarafin jami’an jinya da unguwar zoma, boye bayanan tafiye tafiye daga bangaren marasa lafiya da kuma boye gaskiya adadin mutanen da mutum yayi mu’amala da su.” Inji shi.
Kungiyar ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ma’aikatar kiwon lafiya ta gaggauta sakin albashin jami’an da ta rike wadanda ke aiki a cibiyoyin gwamnatin tarayya.
Haka zalika ya nemi a sake nazari game da albashinsu da hakkokinsu na matakin albashi na COHENSS, kuma a daidaitasu da sauran jami’an kiwon lafiya a matakin albashi wajen daukan aiki.
“An dade da mayar da mu saniyar ware, an hana mu sashin jami’an jinya wanda darakta zai jagoranta, don haka muke kira a habbaka jami’anmu domin su gudanar da bincike.” Inji shi.
Daga karshe ya nemi a shigar da jami’ansu cikin wadanda zasu samu alawus din da ake baiwa duk wadanda suke yaki da COVID19, kayan kariya da kuma inshoran lafiya.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng