Gwamnatin Kano za ta sake mayar da Almajirai 2000 mahaifarsu

Gwamnatin Kano za ta sake mayar da Almajirai 2000 mahaifarsu

Gwamnatin Kano ta kammala shirin sake mayar da wani sabon kashi na Almajirai 2000 da ta killace zuwa jihohinsu kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito.

Kwamishinan ilimi na jihar, Alhaji Sani Kiru, shi ne ya sanar da hakan a ranar Lahadi yayin da ya jagoranci wata tawagar mata ta yada da'awa da kuma wasu kungiyoyi al'umma wajen kai ziyara cibiyoyin killace masu cutar korona a Kiru da Karaye.

Alhaji Kiru wanda kuma ya kasance shugaban kwamitin kula da yashe 'yan makarantun tsangayu daga jihar, ya ce za a mayar da Almajirai 2000 bayan an killace su a cibiyoyin killace masu cutar korona.

Ya ce an killace Almajiran ne domin tabbatar da cewa ba sa dauke da kwayoyin cutar korona gabanin mayar da su jihohin da suka fito.

Bayan tabbatar da koshin lafiyarsu, wadanda suka kasance 'yan asalin jihar Kano kuma su ma za a danka su a hannun iyayensu a cewar kwamishinan.

Kiru ya tabbatar da cewa an samar da ingantattun abubuwan jin dadin rayuwa tare da ciyarwa mai tsabta a cikin dukkanin cibiyoyin killace masu cutar korona dake fadin jihar.

Ya yi tuni a kan yarjejeniyar da gwamnonin Arewa suka kulla na mayar da Almajirai zuwa jihohin da suka fito a yunkurin su na dakile yaduwar cutar wadda ta zamto ruwan daren da ya game duniya.

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje
Source: UGC

A halin yanzu an mayar da daruruwan Almajirai zuwa jihohi da dama na Arewa, haka zalika gwamnatin Kano ta karbi Almajirai da dama da aka dawo da su daga wasu jihohin.

Kwamishinan ya ce nan da kwana biyu zuwa uku, za a mayar da Almajiran da ake killace zuwa tushen da suka fito.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Madagascar ta bukaci Najeriya ta biya kudin maganin da ta aiko

A wani rahoton mai nasaba da wannan, Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya zabge kaso hamsin cikin dari na albashinsa da na dukkan ma su rike da mukaman siyasa da ya nada da wadanda aka zaba a fadin jihar Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wani jawabi da babban mai taimakawa Gwamnan a bangaren yada labarai, Abubakar Aminu, ya fitar ranar Lahadi.

A cikin jawabin, an rawaito gwamna Ganduje na cewa rage albashin ya biyo bayan raguwar da aka samu a kudaden shiga da kasa ke samu saboda kalubalen annobar cutar korona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel