Gwamnati ta garkame wata kamfani da ma’aikatanta guda 30 suka kamu da COVID-19

Gwamnati ta garkame wata kamfani da ma’aikatanta guda 30 suka kamu da COVID-19

Kwamitin yaki da cutar COVID-19 da gwamnatin jahar Oyo ta kafa ta sanar da samun wasu mutane su 30 dake aiki a wani kamfani a jahar sun kamu da cutar Coronavirus.

Jaridar Punch ta ruwaito sakamakon gwaji ya nuna an samu karin mutane 31 da suka sake kamuwa da cutar Coronavirus a jahar, sai dai 30 daga ciki yan kamfani daya ne.

KU KARANTA: Korona: Sabbin mutane 338 sun karu a Najeriya, mutane 64 a Kano

Gwamnan jahar, Seyi Makinde, wanda shi ne shugaban kwamitin ya bayyana haka a shafinsa na Twitter, inda yace kamfanin na karamar hukumar Ibadan ta kudu maso yammacin jahar.

Gwamnan ya bayyana cewa tuni an garkame kamfanin ba tare da wata wata ba, kuma gwamnati za ta yi ma kamfanin feshin magani don gudun yaduwar cutar a jahar.

“Sakamakon gwaje gwajen cutar COVID-19 guda 31 sun fito, kuma sun nuna duka 31 suna dauke da cutar, mutane 30 daga ciki ma’aikatan kamfani daya ne dake karamar hukumar Ibadan maso yamma. Mun kulle kamfanin, kuma zamu tsaftace ta.

“Muna kira ga jama’a dasu kwantar da hankulansu saboda mun shawo kan lamarin, tuni mun fara bin sawun duk mutanen da suka yi mu’amala da ma’aikatan kamfanin, zamu sanar da karin bayani game da matakan daya kamata a dauka.” Inji shi.

Gwamnati ta garkame wata kamfani da ma’aikatanta guda 30 suka kamu da COVID-19
Makinde Hoto: Punch
Asali: Twitter

Gwamnan ya kara da cewa sauran sakamakon gwaji 1 na wani mutum ne daga karamar hukumar Egbeda, don haka adadin masu cutar a jahar Oyo zuwa karfe 8 na daren Lahadi ya kai 107.

Gwamnan ya yi kira ga wadanda suke dauke da alamomin cutar su gaggauta yin rajista ta hanyar kiran waya domin yin gwajin a filin wasa na Adamasingba dake garin Ibadan.

Daga karshe gwamnan ya shawarci jama’a su kai rahoton duk wani bako matafiyi da ya shiga garuruwansu ko unguwanninsu.

Sai dai a hannu guda, hukumar NCDC ta bayyana cewa zuwa karfe 11:20 na daren Lahadi an samu mutane 11 da suka kamu da cutar a jahar Oyo.

Hakan shi ya kawo adadin masu dauke da cutar zuwa 118, sa’annan jahar ta zamo ta 11 a jerin jahohin Najeriya da suka yawan cutar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng