Yanzu-yanzu: Karin mutane 67 sun warke daga Coronavirus, an sallamesu

Yanzu-yanzu: Karin mutane 67 sun warke daga Coronavirus, an sallamesu

Ma'aikatar kiwon lafiyan jihar Legas ta sanar da warkewa da sallamar masu cutar Coronavirus 67 a jihar bayan gwaji biyu a jere ya nuna sun barranta daga cutar.

Ma'aikatar ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita ranar Asabar, 16 ga wtaan Mayu, 2020.

A cewar jawabin, cikin wadanda aka sallama akwai Maza 45 da Mata 22 - wanda ya hada da yan kasar Indiya 2 da dan China 1.

Kawo yanzu, jihar Legas ta sallami mutane 608 masu fama da cutar Korona.

KU KARANTA: COVID-19: Sarkin Daura ya yi nasiha mai ratsa zuciya bayan samun waraka

Jawabin yace: "Masu jinyar cutar COVID19 67; mata 22 da maza45; harda yan kasar waje 3 - Indiyawa 2 da Bachine 1 sun samu sallama daga cibiyoyin killacewanmu."

A ranar 15 ga Mayu, mun samu mutuwar mutane 3. Yanzu adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar COVID19 a Legas ya kai 36.

A yanzu adadin wadanda aka sallama ya hau 608."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel