PDP ta dakatar da Hunkuyi, Dogara da wasu 'ya'yanta 5

PDP ta dakatar da Hunkuyi, Dogara da wasu 'ya'yanta 5

Jam'iyyar PDP ta dakatar da Sanata Suleiman Hunkuyi, Dr Dogara Mato da wasu 'yan jam'iyyar biyar a kan ayyukan zagon kasa ga jam'iyyar a karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Sauran 'yan jam'iyyar da aka dakatar sun hada da Ibrahim Lazuru (karamar hukumar Lere); Dr John Danfulani (karamar hukumar Kachia); Lawal Imam Adamu (karamar hukumar Soba); Ubale Salmanduna (Karamar hukumar Zaria) da Hashim Garba (karamar hukumar Kubau).

Kwamitin ayyuka na jam'iyyar PDP na jihar Kaduna ya yanke hukuncin dakatar da 'ya'yan jam'iyyar bayan binciken farko da ta fara na ladabtar dasu.

PDP ta dakatar da Dogara, Hukuyi da wasu mutum biyar

PDP ta dakatar da Dogara, Hukuyi da wasu mutum biyar. Hoto daga Daily Trust
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Shugaban Guinea Bissau ya kawo ma Buhari maganin Covid-19 na kasar Madagascar (Hotuna)

Kamar yadda takardar ta bayyana a karshen taron kwamitin ayyuka na jihar, sakataren yada labarai na PDP a jihar, Abraham Alberah Catoh ya ce dakatarwar ta biyo bayan biyayya da suka yi ga sashi na 57, sakin layi na 3 na kundun tsarin mulkin jam'iyyar.

Kamar yadda yace, "cewa an dakatar da 'ya'yan jam'iyyar da aka lissafo daga yau 16 ga watan Mayun 2020 kuma ana bukatar su bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa.

"Kwamitin ayyukan ya kara da bayyana cewa Kanal Dauda Albehu Gora bashi da rijistar jam'iyyar don haka bashi daga cikin 'ya'yan jam'iyya.

"Jam'iyyar ta mika sunansa ga jami'an tsaro don su kiyaye. Za mu dauka matakin da ya dace a kan shi idan ya ci gaba da shiga al'amuran jam'iyyar PDP" sakataren yace.

A wani bangare, daya daga cikin dakatattun 'ya'yan jam'iyyar, Dr Danfulani yace, ba a yi masa adalci ba saboda an dakatar da shi ne bayan an zargeshi da aikin zagon kasa ga jam'iyyar amma ba a tsaya an ji ta bakinsa bane.

An yi ta kokarin ji daga ta bakin sauran dakatattun 'ya'yan jam'iyyar amma ba a samu damar hakan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel