Hare-haren 'yan bindiga: Matasa a Katsina sun rufe babban titin da ta sada Najeriya da Nijar

Hare-haren 'yan bindiga: Matasa a Katsina sun rufe babban titin da ta sada Najeriya da Nijar

Mazauna garin Daddara da kauyukan da ke makwabtaka da su a karamar hukumar Jibia a ranar Asabar sun rufe babban hanyar Jibia zuwa Maradi na Jamhuriyar Nijar don yin zanga zanga game da kisan kiyashi da harin da yan bindiga ke musu.

Daruruwan matasa ne suka fito suka tare kofar da ta sada kasashen biyu suna kira ga gwamnatin Najeriya da Nijar su dauki mataki a kan yan bindigan cikin gaggawa.

Sun rufe hanyar da manyan katakai da taya tun misalin karfe 8 na safe, wasu tayoyin ma an banka musu wuta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Matafiya da sauran masu amfani da hanyar duk sunyi carko carko sun gaza wucewa.

Hare-haren yan bindiga: Matasa a Katsina sun rufe babban titin da ta sada Najeriya da Nijar

Hare-haren yan bindiga: Matasa a Katsina sun rufe babban titin da ta sada Najeriya da Nijar. Hoto daga Daily Trust
Source: UGC

DUBA WANNAN: Shugaban Guinea Bissau ya kawo ma Buhari maganin Covid-19 na kasar Madagascar (Hotuna)

Matasan ba su bar wurin ba har da sai da yan sanda da wasu masu sarautun gargajiya suka basu hakuri sannan aka bude hanyar misalin karfe 12 na rana.

Da ya ke magana a kan lamarin, Shugaban Kungiyar Cigaban Daddara, Halilu Buhari ya ce yan bindigan sun kashe musu mutane da dama tare da barnatar musu da dukiya.

Ya ce, kwanaki biyu da suka gabata wasu yan bindigan sun kai hari a Yan Gayya, wani kauye da ke kusa da daji misalin karfe 8 na dare inda suka ci zarafin wasu mata.

A daren ranar kuma, wasu maharan sun kai hari kauyen Zamdam inda suka yi ta jefa banga wadda hakan ya saka firgici a zukutan mutanen kauyen.

"Yan kauyen sun gane cewa ba karar bindiga bace kuma suka fattaki maharan. An yi ta jiran jamian tsaro a waya amma ba su iso a kan lokaci ba, ran mutane ya baci tun lokacin," in ji shi.

Ya cigaba da cewa, hakan ya fusata mazauna kauyen shi yasa suka fita suka yi zanga zanga domin nuna bakin cikin su game da hare haren da ake kai musu a kauyukan.

Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah bai amsa sakon da aka masa ba na neman jin ta bakinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel