Kano: 'Yan sanda sun damke 'yan ta'adda 197 da miyagun makamai

Kano: 'Yan sanda sun damke 'yan ta'adda 197 da miyagun makamai

A kalla mutum 197 ne wadanda ake zargi da laifuka daban-daban da ya hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, satar motoci da kwacen adaidaita ne suka shiga hannun 'yan sandan jihar Kano.

An kama wadanda ake zargin tsakanin ranar 11 ga watan Mayu zuwa 15 ga watan Mayu a yankuna daban-daban na jihar. Rundunar Operation Puff-Adder ne suka yi wannan kamen.

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, jami'in hulda da jama'a na rundunar ya bayyana hakan ga manema labarai a yammacin Juma'a. Ya ce wannan babban ci gaba ne da aka samu.

Ya ce, daga cikin wadanda ake zargin, akwai 'yan fashi da makami 12, masu garkuwa da mutane 5 sai kuma 'yan daba 115.

Bakwai daga ciki masu kwace ne wadanda aka kama da motoci hudu, adaidaita sahu biyu, babura bakwai da kekuna biyu.

Kiyawa ya kara da cewa, hudu daga ciki 'yan kwaya ne da aka kama da sunki 162 na ganye wanda ake zargin wiwi ce. Kudinta kuwa ya kai N810,000 da kuma kwalaye goma na maganin tari mai darajar N935,000.

Ya ce an samu makamai miyagu shida wadanda suka hada da bindiga kirar AK 47, harsasai 321 da sauransu.

Kano: 'Yan sanda sun damke 'yan ta'adda 197 da miyagun makamai
Kano: 'Yan sanda sun damke 'yan ta'adda 197 da miyagun makamai. Hoto daga jaridar The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin tarayya ta bayyana halin da Kano ke ciki

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce akwai yuwuwar hauhawar yawan masu cutar coronavirus a jihar Kano bayan samar da karin dakunan gwajin cutar a jihar.

Ganduje ya sanar da hakan ga manema labarai a yayin ganawa da kwamitin dakile yaduwar cutar coronavirus na Kano a ranar Juma'a, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya ce an kammala shirin samar da dakunan gwaji a kananan hukumomi 36 da ke da nisa da birnin Kano.

"Za mu bude cibiyoyin gwaji a dukkan kananan hukumomi 36 da ke da nisa da birni. Za mu ci gaba da shiri, dole ne mu dauka matakan gaggawa.

"Za mu tabbatar da cewa da cewa dukkan ma'aikatun jihar nan na shirye koda irin wannan halin ko-ta-kwana ya taso," yace.

Ya kara da cewa za su kara kokari wajen tabbatar da an fatattaki annobar kwata-kwata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel